Jerin Hasashe 5 Masu Daga Hankali da Wani Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Game da 2024
- Fasto Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual ya garzaya soshiyal midiya da shafuka 91 na hasashen abun da zai faru a 2024
- Malamin addinin ya yi wasu hasashe masu ban tsoro wadanda suka sako Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata Godswill Akpabio, Nyesom Wike da sauransu
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta tsamo wasu hasashe biyar masu nauyi yayin da 2024 ke gabatowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Fasto Elijah Ayodele, ya bayyana hasashensa game da 2024, kamar yadda yake bisa al'adar malaman addini a kasar.
Hasashen nasa wanda ke kunshe da shafuka 91, dauke da sa hannun hadiminsa, Osho Oluwatosin, malamin ya jaddada bukatar yin addu'a sosai don farfado da tattalin arzikin Najeriya a shekara mai zuwa.
Hasashen ya tabo bangarori da dama kamar siyasa, shugabanci, tattalin arziki, ilimi, wasanni da tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta lissafo wasu hasashe biyar da ya yi wadanda ke cike da damuwa.
1. Rikicin da ke kunno kai tsakanin Tinubu/APC da Wike
Ayodele ya yi ikirarin cewa Allah ya nuna masa cewa banbancin siyasa zai rikida ya koma rikici tsakanin Shugaban kasa Bola Tinubu da Nyesom Wike.
Ya yi hasashen cewa wannan na iya jefa jam'iyyar APC cikin danasanin dauko Wike da suka yi cikinsu.
2. Hasahe kan Nnamdi Kanu
Malamin addinin ya kuma yi hasashe game da fafutukar biyafara, yana mai hango yiwuwar Nnamdi Kanu ya dade a daure.
Bugu da kari, Ayodele ya yi hasashen sabani tsakanin Kanu da Simon Ekpa, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin mabiyansa.
3. Hasashe kan shugaban majalisar dattawa Akpabio
Ya yi hasashen cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio zai fuskanci kalubale daga wasu Sanatoci.
Primate Ayodele ya ce:
"Na ga cewa Sanatoci za su kalli Akpabio ido cikin ido kuma ba za su kalli Akpabio a matsayin mutumin da ke tafiyar da harkokin majalisar dattawa ba.
"Godswill Akpabio ba zai iya cewa komai ba, ciki har da manufofin gwamnati kuma duk abin da gwamnati ke yi, zauisamu karbuwa sosai imma mai kyau ko mara kyau."
A hasashensa, ya shawarci shugaban majalisar dattawan da ya kula da lafiyarsa a cikin watan Agusta, Satumba, da Oktoba.
4. Shirin tsige Nuhu Ribadu
A daya daga cikinhasashen nasa, Primate Ayodele ya ce Allah ya bayyana masa cewa za a yi makarkashiya a karkashin kasa domin tsige mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
Ya ce:
"Allah ya ce yunkurin tsige shi ba zai cimma nasara ba. Za a yi gagarumin yunkuri na yin Allah-wadai da mafi yawan ayyukansa a ofis.
"Ubangiji ya ce akwai bukatar NSA ya kafa sashin leken asiri na malamai domin jagorantar sanar da shiri da umurnin Allah kan tsaron kasar."
5. Rikici a fadar shugaban kasa
Ya yi kira ga yan Najeriya da su dage da addu'a domin hana afkuwar rikice-rikice kamar gobara, hare-hare, ko asarar rayuka a Fadar Shugaban Kasa.
Ya kuma jaddada muhimmancin yin addu’o’i na gama-gari don gujewa mummunan rikicin da ya yi hasashe.
Adeboye ya shawarci yan addu'a kan shugabanni
A wani labarin kuma, mun ji cewa Fasto Richard Adeboye ya shawarci yan Najeriya da su taya shugabannin kasar da addu'a domin samun sauyin da ake muradi.
A cewar Adeboye, zanga-zanga da fadace-fadacen da aka yi a baya ba su sa an yi nasara a kan su ba.
Asali: Legit.ng