Motsi Ya Fi Labewa: Dattawa 250 a Jihar Katsina Sun Samu Tallafi Daga Uwar Gidan Shugaba Tinubu
- Uwar gidan shugaban kasa Tinubu ta sanya farin ciki a zukatan dattawa 250 a jihar Katsina bayan ba su tallafin naira dubu 100 duk mutum daya
- Tallafin naira dubu 100 na daga cikin shirin uwar gidan shugaban kasar na tallafawa dattawa 250 a kowacce jihar Najeriya
- Wannan tallafin zai taimaka wajen rage radadin wahalar da dattawan suka shiga sakamakon janye tallafin man fetur da Tinubu ya yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Katsina - Dattawa 250 ne a jihar Katsina suka amfana da tallafin naira dubu 100 daga shirin uwar gidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu.
Wannan tallafin na daga cikin shirye-shiryen Sanata Oluremi Tinubu na bunkasa rayuwar dattawa a kasar da zai cimma muradin "sabuwar Najeriya".
Manufar shirin ba dattawa tallafin N100,000 a jihohin Najeriya
Dattawan da suka amfana da tallafin sun nuna matukar farin ciki yayin da suka karbi kudin karkashin shirin da zai tallafawa dattawa 250 a kowacce jihar Najeriya. TVC News ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uwar gidan gwamnan jihar Katsina Zulaiha Dikko Umar Radda wacce ta wakilci uwar gidan shugaban kasar ta karfafi guiwar dattawan tare da nuna masu muhimmancinsu a cikin jama'a.
The Nation ta rahoto uwar gidan shugaban kasar na rokon dattawan da su mayar da hankali wajen kula da lafiyarsu da kuma komawa ga Allah don neman lahirarsu.
Tun bayan zuwan gwamnatin Tinubu, ta mayar da hankali wajen bunkasa rayuwar jama'a musamman biyo bayan janye tallafin man fetur da shugaban kasar ya yi.
Tinubu ya dawo da shirin ciyar da dalibai abinci, ya fadi dalili
A wani labarin kuma, shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo da shirin ciyar da dalibai abinci don bunkasa ilimi da rage yawan yara masu gararamba a gari.
Idan ba a manta ba, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya kawo shirin ciyar da abincin, amma ya dakatar da shi bayan dogon lokacin da aka yi ana gudanar da shi.
Sai dai Tinubu ya yi wa shirin garambawul, inda ya dauke shi daga ma'aikatar jin kai zuwa ma'aikatar ilimi don tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ba.
Asali: Legit.ng