Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Jami’in Soja Ya Mutu a Hanyarsa Ta Zuwa Daurin Aurensa

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Jami’in Soja Ya Mutu a Hanyarsa Ta Zuwa Daurin Aurensa

  • Tsohon dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar PRP, Salihu Yakasai, ya nuna alhini kan mutuwar wani sojan Najeriya da ya kwanta dama a hanyarsa ta zuwa aurensa
  • Za a daura auren matashin sojan mai suna Ya'u Yunusa a ranar Asabar ne kamar yadda katin gayyatar aurensa ya nuna
  • Yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi domin nuna alhinunsu kan mutuwar matashin tare da yi masa addu'ar samun rahamar Ubangiji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2023, Salihu Yakasai ya yi alhinin mutuwar wani jami'in sojan Najeriya wanda ya rasu a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa.

Kamar yadda dan takarar gwamnan ya bayyana a shafinsa na X, an shirya za a yi auren sojan mai suna Ya'u Yunusa a ranar Asabar, 23 ga watan Disamba, kafin ya hadu da ajalinsa.

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano sun kama tubabben dan fashi da makami, suna neman wasu 72 ruwa a jallo

Ya yi hatsari a hanyar zuwa bikinsa
Hawaye sun kwaranya yayin da jami’in soja ya mutu a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa Hoto: @dawisu
Asali: Twitter

Yakasai ya nuna alhinin nasa ne a safiyar ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba wanda ya yi daidai da ana gobe daurin auren marigayi Ya'u. Ya rubuta a shafin nasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan ya girgiza ni. Jami'in sojan zai je bikinsa, wanda ke zuwa a ranar Asabar dinnan, ya yi hatsari ne sannan ya mutu. Lallai daga Allah muke, gare shi muke, kuma gare shi za mu koma. Allah ya ji kanka."

Jama’a sun yi alhinin mutuwar jami’in soja

@UsmanZannaah ya yi martani:

“Allah sarki wannan amarya taga mutuwa gaskiya.. Allah ya gafarta masa yasa aljannah ce makomar sa ita kuma amarya Allah ya bata ikon cin jarrabawar nan.”

@RakaFatima ta ce:

“Subhanallah Allah ya jikansa ya gafarta masa.”

@ASMukhtar_ ya yi martani

“Lallai akwai tausayi. Allah yasa ya huta, kuma Allah ya basu hakurin rashi. Ameen”

Kara karanta wannan

Sabon rikici zai kurdo jam’iyyar PDP, Atiku ya lula Dubai bayan shari’ar zabe

@saheedshittu ya ce:

“Inna Lillahi Wahinna Illahi Rajihun. Allah ya gafarta maxi”

@tukur2002ng ya ce:

“Subuhanallh!! Ubangidi Allah ya jikanshi Amin

@HertzHumairah ta ce:

“Idan Allah bai nufa za ka yi aure ba, ba zai taba faruwa va Allah yayi masa gafara Yasa ya huta”

@Nsafiyanu01 ya ce:

“Innalillahi wainna ilaihi Raji un, Allah jikanshi ya gafarta mashi.”

Matashi ya auri mata 2 rana guda

A wani labarin, mun ji cewa wani fitaccen mai watsa shirye-shirye dan kasar Ghana, Michael Houston, wanda ya sha caccaka saboda auren mata biyu a rana daya, ya kare kansa yayin da ya bayyana illar da hakan ya janyo masa.

A kwanan nan ne Houston ya auri Felicity da Khadijah a wani gagarumin biki da aka gudanar, inda hakan ya janyo masa shan caccaka a wajen mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng