Karshen shekara: Manyan Malaman Addinin Musulunci 5 da Suka Rasu a 2023

Karshen shekara: Manyan Malaman Addinin Musulunci 5 da Suka Rasu a 2023

Shekarar 2023 ta zo da abubuwa na ban mamaki waɗanda za su kasance cikin kundin tarihi. A cikin shekarar ta 2023 manyan malaman addinin musulunci sun riga mu gidan gaskiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Rasuwar malaman dai babban rashi ne ga al'ummar musulman Najeriya, duba da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban addinin musulunci.

Malaman addinin musuluncin da suka rasu a 2023
Manyan malaman addinin musuluncin da suka rasu a 2023 Hoto: Abdullahi Bala Lau, Jibwis National HQ Jos
Asali: Facebook

A cikin wannan shekarar akwai aƙalla manyan malaman addinin musulunci guda biyar da suka riga mu gidan gaskiya.

Legit Hausa ta yi duba kan waɗannan malaman da rasuwarsu ta girgiza al'ummar musulmai a shekarar 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sheikh Nasir Muhammad Nasir

A ranar Laraba, 7 ga watan Yuni aka samu labarin rasuwar Sheikh Nasir Muhammad Nasir, wanda aka fi sani da Limamin Waje.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu, Zulum da wasu manyan ƙusoshi da zasu halarci gasar karatun Alqur'ani Mai Girma

Marigayin wanda shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Fagge, ya koma ga mahaliccinsa ne bayan ya kwashe tsawon lokaci yana jinya.

Sheikh Nasir Muhammad Nasir wanda aka taɓa naɗa wa sarautar Wazirin Kano, ya rasu yana shekara 87 a duniya.

2. Sheikh Ibrahim Musa (Albanin Kuri)

A daren ranar Talata, 8 a ga watan Agusta aka samu labarin rasuwar Sheikh Ibrahim Musa, wanda aka fi sani da Albanin Kuri.

Marigayin ya rasunne bayan wasu ƴan ta'adda sun bi shi har cikin gidansa da ke Gombe sun yi masa kisan gilla.

Jaridar Aminiya ta tattaro cewa an yi jana'izar marigayin malamin da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Bolari da ke cikin birnin Gombe.

Miyagun da suka halaka malamin dai sun yi artabu da shi a gidansa, kafin su sassare shi a jiki tare da yanka wuyansa.

3. Sheikh Giro Argungu

A ranar Laraba, 6 ga watan Satumba aka sanar da rasuwar shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Abubakar Giro Argungu, bayan ya yi ƴar gajeriyar jinyar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari kan masu shirin bikin addini a jihar arewa

Shugaban ƙungiyar Izala ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya sanar da rasuwar malamin addinin musuluncin wanda ya rasu yana da shekara 60 a duniya a shafinsa na Facebook.

An yi jana'izar Sheikh Giro a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba a garin Argungu da ke jihar Kebbi.

4. Sheikh Yusuf Ali

Sheikh Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya) ya rasu yana da shekara 73 a duniya. Ya rasu a daren ranar Lahadi, 5 ga watan Nuwamba.

A ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba aka yi jana'izar malamin wanda aka haifa a garin Gaya, a gidansa da ke cikin birnin Kano.

Marigayin ya fara aikinsa a fannin shari'a a shekarar 1974 a kotun shari'ar musulunci a matsayin magatakarda. Sannan ya yi ritaya a shekarar 2009 bayan ya kai matsayin babban darekta a kotun shari'ar musulunci.

5. Imam Sa'id Abubakar

Marigayi Imam Sa'id Abubakar ya rasu a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamban 2023 a birnin Gombe na jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Hukumar NRC ta sanar da fara jigilar yan Najeriya kyauta saboda bikin Kirsimeti da sabuwar shekara

Marigayin mai shekara 71 a duniya, kafin rasuwarsa shi ne babban limamin masallacin Izala na biyu da ke Low Cost a Gombe, cewar rahoton Nigerian Tribune.

An bayyana marigayin a matsayin mutum wanda ya ta'allaka rayuwarsa ga hidimar addinin Musulunci.

Malamin Najeriya Da Ke Aiki a Ka'aba a Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa akwai malamin Najeriya wanda yake aiki a Ka'aba a ƙasar Saudiyya.

Dakta Abdulrahman Sani Yakubu wanda aka haifa a Zariya shi ne shugaban sashen Hausa na masallacin Harami.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng