Tinubu Ya Amince da Nadin Mukamai 46 Bayan Ya Sallami Wasu a Makon Jiya, Bayanai Sun Fito
- Kasa da mako guda bayan korar daraktoci a ma'aikatar harkokin jiragen sama, Tinubu ya maye gurbinsu
- Wannan na zuwa ne mako daya bayan shugaban sallami daraktoci a karkashin ma'aikatar
- Daraktan yada labarai a ma'aikatar, Odutayo Oluseyi shi ya fitar da sanarwar a yau Alhamis 21 ga watan Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Tinubu ya amince da nadin sabbin daraktoci a ma'aikatar harkokin jiragen sama.
Wannan na zuwa ne mako daya bayan shugaban ya sallami daraktoci a karkashin ma'aikatar, Legit ta tattaro.
Yaushe aka sanar da sabbin nade-naden?
Ministan ma'aikatar, Festus Keyamo shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 21 ga watan Disamba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Keyamo ya ce daraktocin su guda 46 sun kunshi hukumomi biyar a ma'aikatar.
Hukumomin da abin ya shafa sun hada da hukumar FAAN da NAMA da NCAA da NSIB da NIMET.
Daraktan yada labarai a ma'aikatar, Odutayo Oluseyi shi ya fitar da sanarwar a yau Alhamis 21 ga watan Disamba.
Wace sanarwa hukumar ta fitar kan nade-naden?
Sanarwar ta ce:
"Duba da shirin Shugaba Tinubu na inganta rayuwar al'umma, Ministan ma'aikatar, Festus Keyamo ya bayyana sunayen dukkan daraktocin.
"Dukkan sabbin daraktocin za su samu daraktan bunkasa ma'aikata don karbar takardar nadin nasu.
"Har ila yau, nadin zai fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba."
Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya kori shugabannin hukumomin FAAN da NAMA da NSIB da NCAA a makon da ya gabata.
Mafi yawan wadanda korar ya shafa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya nada su.
Tinubu ya sallami daraktoci a ma'aikatar jiragen sama
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya amince da korar daraktocin ma'aikatar harkokin jiragen sama.
Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin wadanda su ka hada da FAAN da NAMA da NCAA da NSIB.
Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale a makon da ya gabata.
Asali: Legit.ng