Gwamnan APC Ya Rabawa Ma’aikata N100,000 Don Bikin Kirsimeti
- Gwamnatin jihar Ebonyi ta sha alwashin zama alkhairi ga dukkan ma'aikatan gwamnati a jihar
- Gwamna Francis Nwifuru ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, yayin taron Kirsimeti da aka gudanar a jihar don taya tsoffi da zawarawa murna
- A yayin bikin wanda ya samu halartan Oluremi Tinubu, Nwifuru ya amince da rabawa dukkan ma'aikatan jihar N100,000 a matsayin kyauta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya sanar da batun amincewa da N100,000 a matsayin kyautar Kirsimeti ga daukacin ma'aikatan gwamnati a ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, rahoton Nigerian Tribune.
Nwifuru ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki da dattawan jihar yayin kaddamar da aikin uwargidar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, wanda ya gudana a dakin taro da ke Abakaliki, rahoton Leadership.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Dr. Monday Uzor, babban sakataren labaran gwamnan, Nwifuru ya jaddada cewar albarkatun jihar mallakin mutane ne kuma sakamakon haka, ba za su bari su ci gaba cikin kangin talauci ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Na ji dadin kasancewa cikin wannan shirin. Abin da ya sanar da ni zuwa nan shi ne, babban karamcin uwargidan shugaban kasar Najeriya, mai girma Sanata Oluremi Tinubu.
"Ta nuna za ta iya taimakawa kokarin mijinta a wannan gwamnati.
"Hakki ne da rataya a wuyanmu kuma aikinmu ne taimaka wa mabukata. Kuma na sha fadin haka cewa dole ne mu hada hadu gaba daya domin yin wannan aiki.
"Na ce dole ne ma'aikatan jihar nan su yi rayuwa kamar kowa. Na san babban aiki ne mai wahala, amma dole ayi shi.
"Don haka na yanke shawarar tabbatar da cewa na zama alkhairi ga jihar nan. Ya zama dole a albarkaci kowani iyali ta sanadi na. Kuma dole kowani ma'aikacin gwamnati ya samu naira dubu dari a lokacin nan."
Hakan na zuwa ne bayan matar gwamnan, Misis Uzoamaka Nwifuru ya bayyana cewa mutum 500,000 da suka amfana da shirin za su tafi gida da N100,000 kowannensu da buhun shinkafa.
Tinubu ya isa Lagas bikin Kirsimeti
A wani labarin, mun ji cewa shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dira a jihar Legas yau Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023 domin yin hutun kirsimeti a gida.
Shugaban Ƙasar ya isa jiharsa ne a wani jirgin sama mallakin rundunar sojin saman Najeriya tare da hadimansa.
Asali: Legit.ng