Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Rabewar Najeriya, Ya Bayyana Lokacin da Hakan Zai Faru

Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Rabewar Najeriya, Ya Bayyana Lokacin da Hakan Zai Faru

  • Fasto David Kingleo Elijah na cocin Glorious Mount of Possibility ya ce Najeriya za ta daina zama ƙasa ɗaya kafin babban zaɓe mai zuwa
  • Malamin, a wani faifan bidiyo a shafinsa na YouTube, ya ce ƴan siyasar Najeriya sun riga sun bar 2023 kuma suna aiki domin zaɓen 2027
  • Ko ta yaya, a cewar Elijah, zaɓen ba zai gudana ba kamar yadda mutane za su ce ba za su iya cigaba da zama a tare ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ojo, jihar Legas - A cikin sabbin hasashe na baya-bayan nan, Fasto David Kingleo Elijah, shugaban cocin Glorious Mount of Possibility, ya yi hasashen ƙarshen Najeriya kafin babban zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Manyan hasashen siyada da aka yi wadanda ba su faru ba a 2023

A wani faifan bidiyo da aka wallafa a YouTube a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, malamin ya yi iƙirarin cewa ƴan siyasar Najeriya sun fice daga shekarar 2023 kuma sun riga sun shiga 2027, suna tsara dabarun zaɓe na gaba.

Fasto ya yi hasashen lokacin rabewar Najeriya
Fasto Elijah ya hasaso lokacin da Najeriya za ta rabe Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ƴan siyasar Najeriya sun fice daga 2023 sun koma 2027

Fasto Elijah ya cigaba da cewa siyasa ta fice daga 2023, kuma ya riga ya ga hankalin kowa ya koma 2027, amma a gare shi, sauyi abu ne na tabbas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sun tambayi ko Shugaba Bola Tinubu zai sake tsayawa takara a karo na biyu? Duk da haka, yayin da ƴan siyasa ke tsara dabarun zaɓen 2027, Allah kuma yana yi wa bayinsa dabara.

A cewar malamin, yayin da ƴan siyasa ke shirin tunkarar zaɓen 2027, jama’a sun fusata, suna cewa ba za mu iya cigaba da zama tare ba, sannan za a samu canji.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani matashin ango ya mutu kwana uku kafin ɗaura aurensa

Rayuwa haɗari ce, Fasto Elijah

Shugaban cocin ya ce Allah ya ce masa ya gaya wa kowa cewa rayuwa haɗari ce kuma "duk abin da zai faru gobe ba laifin kowa ba ne".

Fasto Elijah ya kuma yi hasashen cewa za a iya kai wa Isra’ila hari a watan Janairu, kuma hakan na iya jawo yaƙin duniya.

Ya ƙara da cewa Amurka ma za ta iya sauya zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2024, yana mai cewa gagarumin sauyi zai girgiza duniya.

Wannan yana zuwa ne kawai kwanaki 11 zuwa ƙarshen 2023 a yayin da ake cikin ƙalubalen tattalin arziki da yaƙi a duniya.

Ku kalli bidiyon a nan ƙasa:

Fasto Ya Ƙi Karɓar Muƙamin da Gwamna Ya Ba Shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Archbishop Iboyi Godday, ya ƙi amincewa da naɗin da Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi masa a matsayin mamba a hukumar alhazai da walwala ta Kirista.

Faston wanda ya kafa cocin Overflow Chapel da ke Sapele ya bayyana cewa an yi naɗin ne ba tare da amincewarsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng