Inda ranka: Ma'aurata sun sayar da dan su na farko akan bashi a Najeriya
Runduna ta musamman ta 'yan sandan Najeriya a jihar Imo dake a kudu maso gabashin kasar nan sun samu nasarar cafke wasu ma'aurata Ifeanyi Anyanwu da matar sa Amarachi Ugorji bisa zargin laifin sata tare kuma da sayar da wani yaro mai shekara biyu a duniya kan kudi Naira dubu dari 500.
Su dai ma'auratan kamar yadda 'yan sandan suka sanar sun tafka satar ne a karshen watan Agustan da ya gabata a kauyen Umuozu-Uguiri dake a cikin karamar hukumar Isiala Mbano ta jihar.
KU KARANTA: Akwai matsala a zaman Najeriya kasa daya - Ango Abdullahi
Legit.ng dai ta samu cewa kafin wannan lamarin ya faru kuma, ma'auratan sun taba sayar da dan su na fari a bisa bashi zuwa ga wani mutum a garin Fatakwal babban birnin jahar Ribas a shekarun baya.
Da yake karin haske kan lamarin, jami'in hulda da jama'a na hukumar rundunar 'yan sandan jihar SP Andrew Enwerem ya tabbatar da faruwar hakan yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a farfajiyar rundunar a garin Oweri.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng