Yan Majalisa Na Son FG Ta Amince a Rika Cinikayya da Yuan Na Kasar Sin, Sun Bayar da Dalilansu

Yan Majalisa Na Son FG Ta Amince a Rika Cinikayya da Yuan Na Kasar Sin, Sun Bayar da Dalilansu

  • Ƴan majalisa na yin kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki Yuan na ƙasar Sin a matsayin kuɗin musayar kuɗaɗen waje a hukumance
  • Suna ganin idan aka aiwatar da hakan za ta taimaka wa Naira ta dawo da darajar da ta faɗi ƙasa warwas
  • Naira dai ta sha matsin lamba sosai a kasuwar canji inda kullum darajarta ke ƙara raguwa wanda hakan ya sanya tattalin arziƙin ƙasar nan cikin garari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin tarayya ta yi amfani da ƙudirin shekarar 2018 ta amince da Yuan kuɗin ƙasar Sin a matsayin kuɗi wanda za a riƙa gudanar da hada-hadar kasuwanci a Najeriya.

Ƴan majalisar na ganin matakin zai taimaka wajen rage matsin lamba a kan Naira da kuma faɗuwar darajarta.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta kasa ta yi wa Shugaba Tinubu da CBN babbar barazana kan abu 1 tak

Yan majalisa na son a rika amfani da Yuan
Yan Majalisa na son a rika amfani da Yuan na kasar Sin wajen yin cinikayya a Najeriya Hoto: CBN
Asali: Getty Images

Majalisar ta cimma wannan matsaya ne bayan amincewa da ƙudirin da Hon. Jafaru Leko ya gabatar, cewar rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa ƴan majalisar ke son a riƙa amfani da Yuan na China?

Majalisar ta bayar da hujjar cewa idan aka yi la’akari da yawan ciniki tsakanin Najeriya da ƙasar Sin, ya kamata kuɗin ƙasar Sin ya zama asusun ajiyar kuɗaɗen waje a hukumance tare da sauran manyan kuɗaɗen duniya.

A yanzu dai kwamitocin majalisar kan harkokin banki da sauran hukumomin da suka dace za su yi aiki tare da babban bankin Najeriya (CBN), domin zaƙulo hanyoyin da za a bi domin aiwatar da wannan tsarin.

Yuan na ƙasar Sin zai taimaka wa Naira

Da yake magana kan ƙudirin nasa, Leko ya ce tattalin arzikin Najeriya ya samu sauye-sauye masu yawa dangane da darajar Naira, lamarin da ya janyo taɓarɓarewar tattalin arziƙi da rashin tabbas.

Kara karanta wannan

Atiku ya taso Tinubu a gaba, ya yi masa wankin babban bargo kan abu 1

A cewarsa, asusun ba da lamuni na duniya IMF ya gabatar da shawarar karkata asusun ajiyar kuɗaɗen waje ga manyan bankunan ƙasashe masu tasowa ciki har da Najeriya, rahoton The Nation ya tabbatar.

Hon. Leko ya ƙara da cewa, yanayin tattalin arzikin duniya yana samun cigaba, kuma yanayin cinikayyar ƙasa da ƙasa yana canjawa, inda ƙasar Sin ta zama ja gaba wajen harkokin cinikayya a duniya.

Ya ce, ƙasar Sin tana da tsayayyen kudin da aka amince da shi a duniya, wato Yuan (CNY), wanda ke samun karɓuwa a harkokin cinikayyar ƙasa da ƙasa.

Abin da Zai Faru da Tattalin Arzikin Najeriya a 2024

A wani labarin kuma, kun ji Bismack Rewane wani masani a fannin tattalin arziƙi ya yi hasashen yadda tattalin arziƙin ƙasar nan zai kasance a 2024.

Rewane ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta farfaɗo wanda hakan zai sanya a samu sauƙi a kasuwar canji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng