Atiku Ya Taso Tinubu a Gaba, Ya Yi Masa Wankin Babban Bargo Kan Abu 1

Atiku Ya Taso Tinubu a Gaba, Ya Yi Masa Wankin Babban Bargo Kan Abu 1

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben 2023, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya bari kalamansa su yi daidai da ayyukan hukumomin tsaro
  • Atiku ya yi zargin cewa jami’an tsaro sun yi garkuwa da wani marubuci a yanar gizo Precious Eze a gidansa da ke Legas, wanda hakan ya saɓa wa alƙawarin da shugaban ya yi na ƴancin faɗin albarkacin baki da ra’ayi
  • Atiku ya soki kama marubuci a yanar gizon, sannan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta fadawa iyalansa da ɗan Najeriya baki ɗaya dalilin da ya sa aka kama shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya caccaki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan kalaman da ya saba yi.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa na kulla yarjejeniya 8 da Wike", Gwamna Fubara Ya Magantu

Atiku a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Talata, 19 ga watan Disamba, ya ce kalaman shugaban ƙasar na tabbatar da ƴancin faɗin albarkacin baki da mutunta ra’ayin jama’a ya sabawa kamun da aka yi wa Precious Eze kwanan nan.

Atiku ya soki Shugaba Tinubu
Atiku ya caccaki Shugaba Tinubu kan kamun marubuci a yanar gizo Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku ya yi zargin cewa an sace Eze ne a gidansa da ke Legas, kuma jami’an tsaro sun yi shiru har sai da ƴan Najeriya suka fara magana da tambayar inda yake.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Atiku ya fada game da cafke marubuci a yanar gizo

Jigon na PDP yace:

"Babu wani bayani da zai bayyana inda yake da kuma dalilin da ya sa ake tsare da shi har sai da ƴan Najeriya suka fara faɗakarwa kan halin da Precious ke ciki."
"Duk da abin da matashin ya yi, dole ne hukumomin jihar su sanar da iyalansa, abokansa, da kuma ƴan Najeriya haƙiƙanin halin da yake ciki."

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin yan siyasan da suka sanya hannu a yarjejeniya kawo karshen rikicin Rivers

"Wannan ya yi dai-dai da dimokuraɗiyya, ƴancin fadin albarkacin baki da kuma mutunta ƴan jarida su yi ayyukansu na bibiyar abin da gwamnati ke yi ba tare da tsoratarwa ba."

Ƙungiya ta yi kira da a saki Precious Eze

An bayar da rahoton cewa wasu mutanen da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da marubucin na yanar gizo kuma ɗan jarida mai yaɗa labarai. An ce yana da hawan jini kuma yana shan maganin hawan jini.

Ita ma wata ƙungiyar kare haƙƙiin ɗan Adam mai suna RULAAC ta buƙaci a sake shi daga hannun ƴan sanda da hukumomin jihar ke tsare da shi, inda ta ƙara da cewa har yanzu hukumar tsaro ta kasa bayyana laifinsa ga jama’a.

Atiku Ya Magantu Kan Sakin Bayanan Karatunsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya ɗauki zafi bayan wata jarida ta nemi samun bayanan takardun karatunsa.

Atiku ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben watan Fabrairun 2023, ya zargi jaridar da makirci da rashin sanin makamar aiki.

Asali: Legit.ng

Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel