Kasafin 2024: Majalisar Kano Ta Yi Wani Abu da Ya Farantawa Abba Gida-Gida Rai
- Yayin da ake shirin fara sauraron shari'ar gwamnan Kano a Kotun Koli, majalisar jihar ta amince da naira biliyan 437 matsayin kasafin 2024 na jihar
- Tun da fari dai gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya gabatar da naira bikiyan 350 matsayin kasafin, amma majalisar ta mayar da shi naira biliyan 437
- Kakakin majalisar jihar Jubril Ismail Falgore ya dage zaman majalisar har zuwa ranar 29 ga watan Janairu, 2024
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da naira biliyan 437.5 matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2024.
Idan za a iya tunawa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya gabatar da naira biliyan 350 matsayin kasafin kudin a ranar 27 ga watan Oktoba.
Me ya sa majalisar ta kara kasafin kudin daga N350bn zuwa N437.3bn?
Kakakin majalisar jihar, Jubril Ismail Falgore, ya ce an kara kasafin kudin daga naira biliyan 350 uwa naira biliyan 437.3 saboda magance wasu bukatu na jama'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Falgore ya ce za a yi amfani da kaso 64 na kasafin wajen gudanar da manyan ayyuka, sai kuma kaso 38 don gudanar da ayyukan yau da kullum, Daily Trust ta ruwaito.
Majalisar ta gudanar da taron jin ba'asin jama'a kan kasafin a makon da ya gabata, kuma kwamitocin majalisar sun gana da shugabannin kananan hukumomi 44 don kare kasafin su.
Shugaban masu rinjaye majalisar kuma mai wakiltar mazabar Dala, Lawal Hussaini Chediyar, YA ce kasafin zai mayar da hankali kan samar da ingantaccen ilimi, kiwon lafiya, tituna da gine-gine tare da bunkasa mata da matasa.
Majalisar ta dage zamanta har zuwa ranar 29 ga watan Janairu, 2024.
Kotun Koli za ta fara sauraron shari'ar gwamnan Kano
A wani labarin, Kotun Koli ta sa ranar da za ta saurari shari’ar zaben gwamnan jihar Kano na 2023, bayan dogon jira da aka yi,
A rahoton da Daily Trust ta fitar a yammacin Litinin, ta tabbatar da cewa a ranar Alhamis dinnan za a fara sauraron shari’ar.
Abba Kabir Yusuf wanda bai gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ba, ya garzaya kotun koli domin ya iya rike kujerarsa.
Asali: Legit.ng