Inna Lillahi: Mayakan Boko Haram Sun Kai Sabon Farmaki Garin Chibok, Sun Yi Ta’adi
- Mayakan Boko Haram sun kai sabon hari garin Chibok da ke a jihar Borno, inda suka kashe mutum biyu tare da jikkata wasu da dama
- Wani mazaunin garin, Moses Adamu ya ce da yawan 'yan garin sun kwana a cikin dazuzzuka ne saboda kona masu gidaje da 'yan ta'addan suka yi
- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sojoji, 'yan sandan da 'yan sa kai sun kai dauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Chibok, jihar Borno - A ranar Talata ne mayakan Boko Haram suka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama a harin da suka kai garin Chibok da ke karamar hukumar Chibok a jihar Borno.
Garin dai ya fara shahara ne a cikin watan Afrilun 2014 lokacin da maharan suka far wa makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati inda suka yi awon gaba da dalibai sama da 300.
Mazauna garin Chibok sun kwana a dazuzzuka
Harin na baya-bayan nan na ranar Talata ya faru ne da misalin karfe 7 na dare, The Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna yankin, a cewar wani Moses Adamu, sun tsere zuwa dazuzzukan yayin da ‘yan ta’addan suka kai farmakin inda suke harbe-harbe suna kona gidaje tare da kwashe kayan abinci.
Adamu ya ce yawancin mazauna garin sun kwana a cikin dazuzzuka yayin da wasu suka iya samun mafaka a makwabta.
Kokarin da jami'an tsaro suka yi
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce an samu dauki cikin gaggawa daga tawagar hadin gwiwa na sojoji, ‘yan sanda da kuma ‘yan banga na yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth, ya ce:
“Abin takaici, an kashe mutane biyu; Mista Badi, mai shekaru 75, da kuma Ngule, mai shekaru 45, sun mutu a yayin harin."
Sai dai ya ce tuni aka dawo da zaman lafiya a garin.
Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi barna
A wani labarin, akalla mutum shida ne aka yi garkuwa da su yayin da aka kashe mutum daya a wani sabon farmaki da 'yan bindiga suka kai a wani kauyen Sokoto, Legit Hausa ta ruwaito.
Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kai harin inda ta ce maharan sun shiga kauyen Tursa da sanyin safiyar Talata kuma sun yi barna.
Asali: Legit.ng