Shugaba Tinubu Ya Naɗa mutum 11 a Kotun Koli Ana Dab da Yanke Hukunci kan Zaben Gwamnan Kano
- Bola Ahmed Tinubu ya aike da wasika zuwa majalisar dattawa, inda ya nemi ta amince da naɗin sabbin alkalai 11 na kotun koli
- Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya karanta sakon Tinubu wanda ke kunshe da sunayen alƙalai 11
- Wannan mataki na zuwa ne kwana ɗaya gabanin kotun koli ta yi zaman sauraron ƙarar zaben gwamnan Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗin sabbin alƙalai 11 da zasu koma aiki a kotun koli.
Shugaba Tinubu ya nemi amincewa da sabbin alkalan ne a wata wasiƙa da ya aike wa majalisar dattawan, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanto wasiƙar buƙatar Shugaba Tinubu a zaman sanatoci na ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu ya ce buƙatar naɗin alkalan ta yi daidai da tanadin sashe na 231(2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Sunayen alƙalai 11 da aka naɗa a kotun ƙoli
Ya kuma jero sunayen alkalan da yake bukatar naɗawa a kotun koli, wanda suka kunshi, mai shari'a Jummai Sankey, mai shari'a Stephen Adah, da mai shari'a Mohammed Idris.
Sauran sun haɗa da mai shari'a Haruna Tsammani, mai shari'a Jamilu Tukur, mai shari'a Abubakar Umar, mai shari'a Chidiebere Uwa, da mai shari'a Chioma Nwosu-Iheme.
A rahoton Vanguard, ragowar sunayen waɗanda Tinubu ya naɗa a kotun Allah ya isa sune, mai shari'a Obande Ogbuinya, mai shari'a Moore Adumein da kuma mai shari'a Habeeb Abiru.
A gobe Alhamis ne kotun kolin Najeriya ta tsara sauraron shari'ar zaben gwamnan Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf na NNPP da Yusuf Gawuna na APC.
FG zata magance matsalar tsaro a 2024
A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayyan Najeriya ta lashi takobin murkushe matsalar tsaro gaba ɗaya daga nan zuwa 2024.
Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ne ya bayyana haka a wata hira da BBC Hausa wadda aka wallafa ranar Talata, 19 ga watan Disamba, 2023.
Asali: Legit.ng