EFCC Ta Tabbatar da Cewa Tsohon Minista da Ta Ke Nema Ruwa a Jallo Ya Shiga Komarta, Ta Yi Bayani
- Tsohon Ministan wutar lantarki a Najeriya, Olu Ogunloye ya shiga hannun hukumar EFCC
- EFCC a makon da ya gabata ta buga hoton tsohon ministan inda ta ke memanshi ruwa a jallo
- Wata majiya ta tabbatar da cewa hukumar na tsare da Ogunloye tun ranar 13 ga watan Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci a Najeriya (EFCC) ta tabbatar da cewa tsohon ministan wutar lantarki ya shiga hannunta.
Wanda ake zargin, Olu Ogunloye ta shiga hannun hukumar ce kwanaki kadan bayan an ayyana ana nemanshi ruwa a jallo, cewar The Nation.
Mene EFCC ke cewa kan tsohon Ministan?
Wata majiya ta tabbatar wa Channels TV cewa hukumar na tsare da Ogunloye tun ranar 13 ga watan Disambar da mu ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce:
"Tsohon ministan na hannun hukumar tun ranar 13 ga watan Disamba, amma ba a sanar ba ne ga jama'a."
A makon da ya gabata ne hukumar EFCC ta ayyana ana neman tsohon ministan ruwa a jallo kan badakalar makudan kudade.
Mene ake zargin tsohon Ministan da aikatawa?
Ana zargin tsohon karamin Ministan wutar lantarkin ne da badakalar naira biliyan 6 da ya shafi aikin wutar Mambila a jihar Taraba.
Ogunloye ya rike mukamin minista ne a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2023.
An zargi tsohon ministan da karkatar da magudan kudade har biliyan 6 na aikin wutar Mambila da ke jihar Taraba.
Obasanjo ya zargi tsohon ministan da ware wasu kudade ba tare da sanin majalisar zartarwa ba.
Sai dai a bangarenahi, Ogunloye ya musanta zargin inda ya ce tsohon shugaban kasar ya na rikida bayanai kuma ba shi da wata hujja a kan haka.
EFCC ta na neman tsohon minista ruwa a jallo
A wani labarin, Hukumar EFCC ta buga hoto da kuma sunan tsohon ministan wutar lantarki, Olu Ogunloye inda ta ke nemanshi ruwa a jallo.
Ana zargin tsohon ministan da karkatar da naira biliyan shida kan aikin wutar Mambila a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.
Asali: Legit.ng