JAMB: “Ilimi Na Fuskantar Baraza a Najeriya”, Wakilin Dalibai Ya Nemi Alfarma Wurin Tinubu

JAMB: “Ilimi Na Fuskantar Baraza a Najeriya”, Wakilin Dalibai Ya Nemi Alfarma Wurin Tinubu

  • An yi kira ga Shugaba Tinubu da ya ba da umurnin janye batun karin kudin jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) don bunkasa ilimi a kasar
  • Wakilin Daliban Durbin Katsina, Sanusi Yau Mani ya yi wannan kiran a zantawarsa da Legit Hausa inda ya ce ya kamata ilimi ya zama kyauta a Najeriya
  • Sanusi Mani ya ce har sai an samar da ilimi ga matasa ne za a kawo karshen ta'addanci a kasar, yana mai cewa bai kamata ayi wasa da harkar ilimi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - An bayyana karin kudin jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) da hukumar JAMB ta yi matsayin barazana ga ilimi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Babban hafsan tsaro CDS ya faɗi halin da ake ciki a bincike kan jefa Bam a taron Musulmai a Kaduna

Wakilin Daliban Durbin Katsina, Sanusi Yau Mani, ya bayyana hakan a zantawarsa da Legit Hausa inda ya ce za a kara samun yawaitar zauna gari banza saboda karin kudin jarrabawar.

An roki Tinubu ya mayar da ilimi kyauta a Najeriya
Wakilin daliban ya ce kamata ya yi ace ilimi ya zama kyauta a Najeriya tare da tilasta shi akan duk wani dan kasar. Hoto: @officialasiwajubat, @MrSymani
Asali: Facebook

Abin da Wakilin Dalibai ya ce game da kara kudin JAMB

Mr. Sanusi Mani ya ce kamata ya yi ace ilimi ya zama kyauta a Najeriya tare da tilasta shi akan duk wani dan kasar kamar yadda aka yi a zamanin baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Ba mu ji dadin karin kudin da hukumar JAMB ta yi ba, domin hakan na nufin dalibai da dama ba za su samu damar ci gaba da karatu a manyan makarantu ba.
"Babu wani abu da za a yi wa talaka na azo a gani da ya wuce saukaka masa ta fuskar ilimi, amma karin kudin jarrabawar JAMB tsari ne da zai cutar da fannin ilimi a kasar baki daya."

Kara karanta wannan

Jami'in NSCDC da ya yi suna kan katobarar 'Oga at the Top' ya samu karin girma, an tuna baya

Wakilin Dalibai yaroki Tinubu ya mayar da ilimi kyauta

Wakilin daliban ya yi nuni da cewa, ma'aikatu da hukumomi na rige-rige wajen tara kudaden shiga don burge gwamnatin tarayya, amma bai kamata a yi wasa da ilimin 'yan Najeriya ba.

"Ba abin burge wa ba ne ace hukumomin da suka shafi ilimi su shiga sahun rige-rigen tarawa gwamnati kudi ba, duk hukumar da ke haka to ta sani ta dauki hanyar gurguntar da rayuwar jama'a ne.
"Mafi akasarin yaran da suka addabi jama'a a gari su ne wadanda ba su samu damar yin karatu ba, ya kamata ilimi ya zama kyauta kuma wajibi kan kowanne dan Najeriya, hakan zai kawo sauyi mai yawan gaske"

Mr. Sanusi Mani ya ce gwamnati ta dade ta na kawo tsare-tsaren da ke cutar da jama'a maimakon saukaka masu, inda nuna bukatar samun sauyin hakan a gwamnatin Shugaba Tinubu.

Ya yi kira ga hukumar JAMB da gwamnatin tarayya da ma masu ruwa da tsaki da su taimaka wa dalibai don yin karatu mai zurfi, a cewarsa hakan ne kawai zai rage yawan ta'addanci a kasar.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

JAMB ta kara kudin zana jarrabawar UTME daga 2024

A jiya ne Legit Hausa ta ruwaito maku sanarwar hukumar JAMB ta kara kudin zana jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) da zai fara aiki daga shekarar 2024.

Hukumar ta mayar da kudin zuwa naira 7,700 ga masu son zana UTME tare da jarrabar gwaji (mock), da kuma naira dubu 6,200 ga masu son zana UTME ba tare da jarrabawar gwaji (mock) ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.