Tsaka Mai Wuya: Sama Da ’Yan Najeriya 1,000 Aka Damfara da Sunan Sama Masu Aiki a Burtaniya

Tsaka Mai Wuya: Sama Da ’Yan Najeriya 1,000 Aka Damfara da Sunan Sama Masu Aiki a Burtaniya

  • Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi 'yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan yayin da suke fafutukar neman ayyukan yi a kasashen waje
  • Shugaban hukumar IOM na majalisar ya ce yanzu haka akwai sama da 'yan Najeriya 1,000 da aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya
  • Mr Boeck ya bayyana cewa masu damfarar kan ba mutum takardun daukar aiki na bogi, sai mutum ya je kasar ya gane kuskuren da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar kula da 'yan ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM), ta ce sama da ‘yan Najeriya 1,000 ne suka fada komar 'yan damfara da ta shafi neman guraben ayyukan yi a Burtaniya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, sun yi mummunar barna

Shugaban hukumar ta IOM, Laurent De Boeck ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai jiya a Abuja.

Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya
Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya. Hoto: @IOM_Nigeria
Asali: Twitter

A rahoton Vanguard, Boeck ya yi nuni da cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun yi asarar kusan dala 10,000 kowannensu a kokarinsu na neman samun ayyukan yi a kasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ake damfarar mutane da sunan sama masu aiki - Boeck

Ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su na watangaririya ne a Burtaniya saboda ba su da hanyar dawowa gida, wasu kuma suna jin kunyar komawa ga iyalansu hannu rabbana, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa:

"Akwai wasu daga cikinsu da suka yi asarar sama da dala 10,000 da aka ba su takardun aikin bogi da suka basu damar samun biza.
“Da suka isa wurin, suka gabatar da takardun, kamfanonin suka gaya musu cewa ba su da masaniya kan wadannan takardun daukar aiki."

Kara karanta wannan

Duka yarjejeniya 8 da aka dauka wajen sasanta Wike da Gwamna Fubara a Aso Rock

Boeck ya kara da cewa IOM na kokarin dawo da dubunnan mutane da suka hada da ‘yan Najeriya daga kasar Tunisiya, wadda a baya-bayan nan ta sanya dokar hana ci-rani a kasar.

Burtaniya ta bude kofar tallafa wa daliban Najeriya

A wani labarin, dalibai daga Najeriya da wasu kasashe 14 sun samu damar neman tallafin karatu daga gidauniyar GREAT gabanin zangon karatu na shekarar 2024-25.

Tallafin zai ba daliban Najeriya da sauran kasashen damar samun Euro 10,000 don biyan kudin makaranta a shirye-shiryen karatu na matakin PGD a jami'o'in Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.