Brexit ba zai hana Birtaniya tarbar ‘Yan ci-ranin Afrika ba Inji Boris

Brexit ba zai hana Birtaniya tarbar ‘Yan ci-ranin Afrika ba Inji Boris

Boris Johnson, Firayim Ministan Birtaniya ya ce kasarsa za su rika tarbar ‘Yan Afrika hannu biyu-biyu duk da shirin ficewarta daga cikin kungiyar kasashen Turai.

Firayim Ministan ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afrika a babban taron Ingila da mutanen Nahiyar da aka soma a Landan.

Johnson ya gana da shugabannin Najeriya wanda su ka hada da Abdel Fattah Al-Sisi na kasar Masara da Muhammadu Buhari na Najeriya a babban Birnin Landan dazu.

Shugaban Birtaniyan ya shaidawa shugabannin na Nahiyar Afrika cewa ya na da burin ganin kasar Ingila ta zama ‘Yaruwar Afrika wajen harkar kasuwanci da zuba jari.

Ana wannan taro ne yayin da makonni biyu kacal su ka ragewa kasar Birtaniya ta fice daga EU. Kasar ta dauki matakin ficewa daga karkashin lemar kungiyar EU ta Turai.

KU KARANTA: Kotun koli: Manyan Jam'iyyar PDP sun fara zanga-zanga a Najeriya

Brexit ba zai hana Birtaniya tarbar ‘Yan ci-ranin Afrika ba – Inji Boris
Buhari da Takwarorinsa wajen taron kasashen Afrika da Ingila
Asali: Twitter

Johnson ya ke cewa akwai adalci a tsarin ci-ranin karbar ci-rani a Birtaniya inda su ke maraba da Bayin Allah daga kowane yankin Duniya su ka fito, har da Afrika.

“Wajen la’akari da mutane kafin kula da fasfon kasarsu, za mu jawo duk wasu masu basira da ake ji da su a Duniya, a ko ina su ke." Johnson ya fadawa Nahiyar Afrikan.

A na sa bangaren, shugaba Muhammadu Buhari, ya ce shirin Brexit ya ba kasashen da ke tare da Ingila a karkashin inuwar Commonwealth karin damar huldar kasuwanci.

Sai dai ‘Yan Afrika su na fama da kalubale wajen samun takardun shiga kasar Ingila a cewar shugaban Najeriya. Buhari ya ce ‘Yan Afrika ba su jin ana yi da su a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel