Gwamna Ya Gabatar da Kasafin Kudin da Ya Sha Gaban na Kowace Jihar Arewacin Najeriya
- Mai girma Sanata Uba Sani ya samu gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a zauren majalisar dokokin jihar Kaduna
- Gwamnan Kaduna ya nemi amincewar ‘yan majalisar dokoki domin ya kashe N458bn a shekarar 2024 da za a shiga
- Abin ban sha’awa a kasafin na 2024 shi ne yadda aka ware makudan biliyoyi domin a inganta harkar ilmi a Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - Mai girma Uba Sani ya gabatar da kundin kasafin kudin shekarar 2024 gaban majalisar dokoki domin a amince da shi.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya tabbatar da haka a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.
Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya batar da N458.3bn a shekara mai zuwa, abin da ya rage shi ne ‘yan majalisar dokoki su amince.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda za a kashe N458bn a Kaduna
Legit ta fahimci kusan 70% na kasafin (N318.8bn) za su tafi ne wajen ayyuka, za a kashe 30.4% (N139bn) a harkokin yau da kullum.
Ilmi ya samu N115b (25.19%); kiwon lafiya N71.6b (15.63%) sai harkar gona, ayyuka, gina abubuwan more rayuwa N93.5b (20.42%).
Gwamna Uba Sani ya ce kasafin na 2024 zai maida hankali wajen raya karkara domin toshe gibin da ke tsakanin kauyuka da birane.
Kamar yadda gwamna ya nemi alfarma, mukaddashin shugaban majalisa, Henry Danjuma Magaji ya ce za a amince da kasafin da wuri.
Kasafin kudin sauran Jihohin Arewa
Zuwa yanzu wannan ne kasafin kudin da ya fi na kowace jiha a yankin Arewacin kasar.
Jihar Katsina wanda ta shirya kasafin N453bn na biye, sai gwamnatin Abba Kabir Yusuf da ta gabatar da kasafin N350bn a jihar Kano.
Gwamna Babangana Zulum zai so kashe N340bn a 2024 yayin da Bala Mohammed ya gabatar da kundin kasafin N300bn ga majalisa.
Gwamnan Kwara ya bukaci majalisa ta amince a kashe N296bn, Filato za ta kashe N296bn, Adamawa tayi kasafin N250bn domin badi.
Gwamnoni suna jiran FAAC
Ana da labarin yadda rahoton ASVI ya fallasa Jihohin kasar nan. An fahimci Gwamnoni kusan 60 duk sun zama ci-ma-zaune ne.
Mafi yawan jihohi suna jiran ayi rabon FAAC ne, Legas kadai ta tattara fiye da 30% na kudin da duka Jihohi 36 su ka iya tatsowa a 2022.
Asali: Legit.ng