Kotu Ta Haramtawa Ministar Shugaba Buhari Sake Rike Mukamin Gwamnati a Najeriya
- Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ta karbi karar da kungiyar NBA ta shigar a kan Pauline Tallen
- Kungiyar lauyoyin Najeriya ta maka tsohuwar Ministar a kotu saboda ta soki hukuncin da kotu ta yi a baya
- Saboda haka Alkali ya zartar da hukunci cewa dole ta nemi afuwa, ko kuwa ba za ta sake iya rike mukami ba
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
FCT, Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta haramtawa Pauline Tallen rike wani mukami na gwamnati a kasar nan.
Rahoton da aka samu daga Premium Times ya tabbatar da kotu ta yanke hukunci ne a kan Madam Pauline Tallen a ranar Litinin.
Alkali ya samu tsohuwar Ministar harkokin mata da cigaban al’ummar da kalaman da su ka soki wani hukunci da kotu ta zartar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifin mene Pauline Tallen ta aikata?
Abin da ya faru kuwa shi, wata kotun tarayya mai zama a garin Yola ta soke takarar Aishatu Dahiru Binani kafin ayi zaben 2023.
Wannan hukunci da kotun tarayya ta yi na hana Sanatar zama ‘yar takarar gwamna a zaben Adamawa bai yi wa Tallen dadi ba.
Saboda haka ne tsohuwar Ministar matan ta ce hukuncin banza aka zartar, maganar da ba tayi wa lauyoyi da alkalan kotu dadi ba.
Tallen tayi kira ga jama’a su yi watsi da hukuncin da aka zartar a kan Sanata Aisha Binani.
Kungiyar NBA ta kai Tallen kotu
Rahoto ya ce saboda haka ne Yakubu Maikyau a matsayinsa na shugaban kungiyar NBA, ya bukaci ‘yar siyasar ta fito ta nemi afuwa.
Tsohuwar mataimkiyar gwamnan ta jihar Filato ba ta bada hakuri kamar yadda NBA ta nema, a dalilin haka kungiyar ta kai ta kotu.
Da aka yi hukunci, kotu ta ce kalaman Tallen sun saba doka, kuma akwai ganganci da takaici da kuma rashin yi wa bakinta linzami.
Idan Tallen ba ta bada hakuri a gidajen jaridu biyu nan da kwana 30 ba, kotu ta ce hukuncin hana ta rike mukami zai fara aiki.
Tinubu ya sasanta Wike da Fubara
Ba tare da bata lokaci ba, an samu labari dole Gwamnan Ribas zai janye karar da ya shigar gaban kotu kan rikicin jihar da ake yi.
Nyesom Wike da ‘Yan Majalisa sun samu yadda su ke so, za a maido Kwamishinonin da su ka sauka, amma ba za a tsige gwamna ba.
Asali: Legit.ng