Za a samu sauye-sauye a harkokin mata, in ji Tallen
Sabuwar ministar harkokin mata da ci gaba jama’a, Pauline Tallen, ta bayyana cewa za a ga sauye-sauye masu inganci a ma’aikatar domin ci gaban mata, yara da kuma marasa galihu a kasar.
Da take jawabi ga ma’aikatan ma’aikatar a lokacin da ta karbi aiki a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, ta bayyana ma’aikatar a matsayin cikakken aiki sannan ta basu bayanin yiwuwar chanje-chanje da za a samu a cikinta.
Ta bayyana cewa mata sun kasance tubalin kawo ci gaba a cikin al’umma, cewa ya zama dole a tafi da su wajen tsare-tsare da zartar da hukunci kan tattalin arziki da sauran manufofin ci gaba.
Tallen ta kara da cewa dukkanin ministoci sun yanke shawarar yin aiki a matsayin tawaga guda tare da Shugaban kasa, inda ta kara da cewa ma’aikatar ta kasance bankasasshiya sannan kuma cewa tana da hakoki da dama akanta na sauyya rayuwar marasa galihu, yara da kuma mata a kasar.
KU KARANTA KUMA: Ba zan lamunci rashin da’a ba, ministan noma ya yi gargadi
A baya Legit.ng ta rahoto cewa ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya yi alkawarin kara kaimi da kuma tabbatar da yardar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake daura masa a karo na biyu.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Mohammed yayi alkawarin ne a Abuja a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, a taron fara aiki wanda sakatariyar din-din-din ta ma’aikatar ta shirya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng