Gwamnan PDP Ya Shiga Matsala Bayan Kotu Ta Sake Rufe Asusun Bankunan Jihar 10, Ta Fadi Dalilai

Gwamnan PDP Ya Shiga Matsala Bayan Kotu Ta Sake Rufe Asusun Bankunan Jihar 10, Ta Fadi Dalilai

  • Gwamna Seyi Makinde ya shiga matsala bayan kotu ta rufe dukkan asusun bankunan gwamnatin jihar guda 10 a fadin kasar
  • Kotun ta umarci dukkan bankunan da abin ya shafa da su halarci zaman kotun na gaba don ba da bahasi kan rashin biyan kudaden
  • Wannan na zuwa ne bayan tsaffin ciyamomin kananan hukumomi sun shigar da gwamnan kara kan basukan naira biliyan 4.9

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin rufe asusun bankunan gwamnatin jihar Oyo 10 a fadin kasar.

Wannan umarni na kunshe ne a cikin hukuncin kotun da Mai Shari'a, Anitte Ebong a yau Litinin 18 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

APC ta yi nasara yayin da kotu ta dakatar da INEC kan sake zaben 'yan Majalisu 27, ta tura gargadi

Kotu ta rufe asusun bankunan gwamnatin jihar PDP saboda basuka
Kotu ta rufe asusun bankunan gwamnatin jihar Oyo kan basukan biliyan 3.5. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Wannan na zuwa ne bayan tsaffin ciyamomin kananan hukumomi sun shigar da gwamnan kara kan basukan naira biliyan 4.9, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya sallami ciyamomin ne wadanda 'yan jami'yyar APC ne a ranar 29 ga watan Mayun 2019 bayan hawanshi karagar mulki.

Tsaffin ciyamomin wanda Bashorun Majeed Ajuwon ke jagoranta sun bukaci a biya su basukan biliyan 3.5 bayan Makinde ya biya biliyan 1.5 a 2022.

Daga cikin bankunan da aka rufe akwai UBA da First Bank da Wema da Zenith da GT Bank da Access da Ja'iz da Polaris da sauransu.

Wane umarni kotun ta bai wa bankunan?

A yayin hukuncin, Ebong ya umarci dukkan bankunan su halarci zaman kotun na gaba don ba da bahasi kan kin biyan kudaden.

Alkalin ya kuma umarci biyan naira dubu 300 ga wadanda ke bin bashin, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Jigon LP ta bayyana wanda ya kamata Kotun Koli ta ayyana a matsayin gwamnan Kano

Har ila yau, ya dage ci gaba da sauraran shari'ar har sai ranar 5 ga watan Janairun 2024 mai zuwa.

A watan Mayun 2021, Mai Shari'a, Ejembi Eko ya yi hukunci inda ya yi fatali da matakin da Makinde ya dauka na korar tsaffin ciyamomin daga kujerunsu.

Kotu ta umarci Makinde biyan bashin biliyan 3.5

A wani labarin, Kotu ta umarci Gwamna Seyi Makinde da ya gaggauta biyan basukan ciyamomin kananan hukumomi naira biliyan 3.5 da su ke bin shi.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya kori ciyamomin a kujerunsu a ranar 29 ga watan Mayun 2019 bayan ya hau karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.