Assha: Gobara Ta Tashi a Gidan Tsohon Gwamna, Mutum Biyu Sun Mutu
- Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta tabbatar da cewa gobara ta lakume gidan tsohon gwamnan Oyo, marigayi Adebayo-Akala
- Wani wanda gobarar ta tashi gabansa ta shaida wa manema labari cewa mutum biyu sun mutu yayin da aka garzaya da wani asibiti
- Sai dai har zuwa yanzu ba a gano musabbabin abin da ya haddasa gobarar ba, inda hukumar kashe gobarar ta ce tana kan bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Oyo - Akalla mutum biyu suka mutu a wata gobara da ta tashi a gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala.
Kwamandan hukumar kashe gobara na Obomoso, Mr Oluwaseyi Awogbile, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda gobarar ta fara karfe 7:30 na safiyar Litinin, 18 ga watan Disamba, 2023.
Barnar da gobarar ta yi a gidan
Har yanzu ba a samu musabbabin faruwar lamarin ba, sai dai Leadership ta tattaro vewa tangardar wutar lantarki ce ta yi sanadin tashin gobarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mr. Awogbile ya ce har yanzu suna gudanar da bincike kan abin da ya haddasa gobarar, inda wani ganau ya tabbatar da cewa mutum biyu sun mutu a cikin gobarar.
Ganau din ya kuma shaida cewa mutum daya ya samu rauni inda aka garzaya da shi asibiti don nema masa lafiya.
Gobara ta babbake babbar kasuwar Kabba, jihar Kogi
A wani labarin, wata gobara da ta tashi a Asubahin ranar Litinin, ta jawo asarar miliyoyin naira a wani bangare na babbar kasuwar Kabba a jihar Kogi.
Gobarar ta lakume shaguna masu tarin yawa, yayin da ta bar 'yan kasuwa da mazauna yankin cikin tashin hankali, babu wanda ya iya shawo kanta.
Shugaban majalisar dattawa ya yi magana kan rade-radin ya yanke jiki ya fadi a bikin cika shekaru 61
Yunkurin kashe gobarar ya ci tura, yan kasuwa sun saduda
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5 na Asuba, inda ta mamaye kasuwar tare da cinye shaguna masu yawa.
Kokarin jama'a na kai dauki don kashe gobarar tare da dakileta daga yaduwa ya ci tura, ana kashe ta kamar ana kara rura ta ne, ta gagari kowa.
Wani da abin ya faru gaban idonsa ya ce haka 'yan kasuwa suka saduda, suna kallo kayansu na ci da wuta amma babu wanda zai iya yin wani abu akai.
Asali: Legit.ng