Hukumar JAMB Ta Yi Karin Kudin Jarrabawar UTME Na Shekarar 2024, Dalibai Sun Koka

Hukumar JAMB Ta Yi Karin Kudin Jarrabawar UTME Na Shekarar 2024, Dalibai Sun Koka

  • Wani sabon rahoto ya yi nuni da cewa hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta kara kudin UTME
  • Sabon kudin da dalibai za su biya don zana UTME zai fara ne daga shekarar 2024, inda karin ya shafi jarrabawar mai hade da gwaji (mock) da maras gwaji
  • Sai dai dalibai sun nuna rashin jin dadinsu kan wannan karin, inda suke ganin wannan ba lokacin da ya kamata hukumar ta yi karin kudi ba ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta kara kudin rijistar jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME) na shekarar 2024.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta JAMB ta fitar, ta bayyana cewar sabon farashin kudin rijistar jarrabawar zai fara aiki shekara mai kamawa.

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa Na 2027: An Zargi El-Rufai da Shirya Tuggu Don Kawo Cikas Ga Gwamnatin Tinubu

JAMB ta kara kudin jarrabawar UTME 2024
Hukumar JAMB ta kara kudin rijistar jarrabawar shiga manyan makarantu (UTME) na shekarar 2024. Hoto: Jambadmin
Asali: Facebook

Nawa ne JAMB ta kara a kudin jarrabawar?

Ga yadda karin kudin ya kasance:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naira 7,700 ga masu son zana UTME tare da jarrabar gwaji (mock), da kuma naira dubu 6,200 ga masu son zana UTME ba tare da jarrabawar gwaji (mock) ba.

The Guardian ta rahoto cewa a baya dalibai na biyan naira 6,700 don zana UTME tare da jarrabawar gwaji, yayin da su ke biyan naira 5,700 don zana UTME ba tare da jarrabawar gwaji ba.

Haka zalika hukumar JAMB ta ce yanzu daliban kasashen waje da ke son zana jarrabawar za su biya dalar Amurka 30.

Rahoton Channels TV ya yi nuni da cewa zuwa nan da ranar 15 ga watan Janairu, 2024 ake sa ran JAMB za ta bayar da cikakken bayani kan karin kudaden da ta kara.

Kara karanta wannan

Jami'in NSCDC da ya yi suna kan katobarar 'Oga at the Top' ya samu karin girma, an tuna baya

Dalibai sun koka kan karin kudin JAMB

Sai dai wannan karin kudin da JAMB ta yi bai yi wa dalibai dadi ba, inda mataimakiyar shugaban daliban jami'o'in birnin tarayya Abuja, Zainab Abdullahi Dass, ta ce bai kamata hukumar ta yi karin kudi yanzu ba.

A zantawarta da Legit Hausa, Zainab Dass ta ce dalibai da dama ba sa iya biyan kudin jarabawar a yanzu saboda "talaucin da ake fama da shi a kasar", wanda wannan karin zai kara yawan marasa zuwa makaranta.

A cewar ta:

"Ya kamata ace hukumar ta rage kudin zana jarabawar don baiwa kannen mu da suka kammala sakandire damar zuwa makarantar gaba.
"Amma wannan karin na naira dubu daya da ka raina, zai tilasta dalibai da yawa hakura da zana jarabawar, dama can ya aka kare balle yanzu an yi karin kudin?"

Mataimakiyar shugaban daliban, ta yi kira ga hukumar da ta sake duba batun karin kudin, tare da yin kira ga gwamnati da ta kawo tsarin tallafawa dalibai masu shirin zana jarabawar JAMB din.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fara shirin tsige gwamna daga kan madafun iko kan abu 1 tal

WAEC ta fito da sabon tsarin rubuta jarrabawar na zamani

A wani labarin, hukumar zana jarabawar kammala karatun sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC), ta sanar da kawo tsarin amfani da kwamfuta (CBT) don zana WASSCE .

A cewar hukumar, za ta fara amfani da sabuwar fasahar ne ga daliban da za su zana jarrabawar WASSCE masu zaman kansu a watan Fabrairun 2024.

Tuni dai kowa ya sani hukumar shirya JAMB ta kawo canjin tsara gudanar da jarrabawar da take yi ga dalibai masu shiga jami'a (UTME) daga takarda zuwa tsarin CBT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.