A mayar da hukumar Hisbah da Amotekun su zama 'yan sandan jiha - Akinrinade

A mayar da hukumar Hisbah da Amotekun su zama 'yan sandan jiha - Akinrinade

- A mayar da hukumar Hisbah da Amotekun su zama 'yan sandan jiha

- Hakan ya fito daga bakin tsohon shugaban ma'aikata na hukumar tsaron Najeriya, Lt. Gen. Alani Akinrinade

- Ya ce dole gwamnati ta bari a gabatar da 'yan sandan jiha matukar ana son dawowar zaman lafiya a Najeriya

Tsohon shugaban ma'aikata na hukumar tsaro ta Najeriya, Lt. Gen. Alani Akinrinade, ya shawarci gwamnatin tarayya ta kyale hukumomin Hisbah dana Amotekun da su zama 'yan sandan jiha.

Haka kuma ya bukaci a sanya dokoki da ya kamata 'yan sandan jihar su dinga bi idan aka basu wannan dama.

A mayar da hukumar Hisbah da Amotekun su zama 'yan sandan jiha - Akinrinade
A mayar da hukumar Hisbah da Amotekun su zama 'yan sandan jiha - Akinrinade
Source: Twitter

Akinrinade ya bayyana haka ne a ranar Asabar a gidansa dake Yakoyo, jihar Osun, a lokacin da yake karbar bakuncin wata tawaga da taje masa ziyara daga ma'aikatar kimiyya da fasaha ta jiha, wacce mai bawa gwamna Adegboyega Oyetola shawara, Mr Olatunbosun Oyintiloye ya jagoranta.

A wata sanarwa da Oyintiloye ya fitar a ranar Lahadi, Gen Akinrinade ya bayyanawa jaridar PUNCH a Osogbo cewa, ya bukaci gwamnati ta amince da 'yan sandan jiha domin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Ya kara da cewa kokarin da ake yi na kawo karshen ta'addanci a Najeriya dole ne ayi shi a tsakanin al'umomin yanki ba wai ayi shi kamar yadda aka saba ba.

KU KARANTA: An bawa gwamnan jihar Zamfara babbar sarauta a kudancin Najeriya

Akinrinade ya roki gwamnatin tarayya tayi na'am da tsarin 'yan sandan jihar, ta hanyar bawa duka hukumomin da suke zaman kansu irin su Hisbah dake yankin Arewa, Amotekun dake yankin Kudu maso Yamma, da dai sauransu.

Da yake magana akan sanya Amotekun a matsayin 'yan sandan jihar, Akinrinade ya ce kada jiha tayi tunanin za ta yi amfani da kudinta wajen tafiyar da wannan hukuma.

Ya bukaci cewa dole ne a bari kowacce jiha ta dauki nauyin 'yan sandan ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel