An Yi ‘Kare-Jini Biri-Jini’ Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ’Yan Ta’adda Sun Bakunci Kiyama

An Yi ‘Kare-Jini Biri-Jini’ Tsakanin Boko Haram da ISWAP, ’Yan Ta’adda Sun Bakunci Kiyama

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda fada ta barke tsakanin ISWAP da Boko Haram a cikin kwanakin nan
  • An ruwaito am kashe akalla 'yan ta'adda 40 a farmakin da suke kaiwa juna tsakanin 15 - 17 ga watan Disamba
  • Gaba na ci gaba da tsami tsakanin 'ya ta'addan biyu da suka rabe gari a shekarun da suka shude can baya

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Jihar Borno - Kungiyar Boko Haram ta sha kashi da ba a taba ganin irinsa ba daga ISWAP a cikin makon da ya wuce, inda gaba ta kara tsananta artabu tsakanin 'yan ta'addan.

An tattaro cewa, sabon farmakin ya kai ga tarwatsa kungiyar Boko Haram ta tsagin Buduma a Tumbum Ali da Kadunan Ruwa a karamar hukumar Kukawa.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Wata mata ta hango alheri bayan da Dangote ya samu kishiya wajen gina matatar mai

An yi kare-jini tsakanin Boko Haram da ISWAP
'Yan Boko Haram da ISWAP sun yi kashe-kashen juna | Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Zagazola Makama ya fahimci cewa kafin janyewar mayakan Boko Haram, gungun 'yan ta'addan biyu sun shafe kusan kwanaki biyu suna gwabza kazamin fada tsakanin 15 ga watan Disamba zuwa 17 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaki ya yi tsami tsakanin Boko Haram da ISWAP

An hango mayakan ISWAP a cikin Marte suna tura karin mayaka dauke da muggan makamai a cikin kwale-kwale zuwa yankunan da mayakan Boko Haram ke da iko da su.

A ranar 17 ga watan Disamba, rahotanni sun ce ISWAP ta mamaye mayakan JAS, inda ta tilasta musu tserewa zuwa bakin Kala a Marte yayin da wasu da dama suka tsere zuwa Darak da ke kan iyakar Kamaru.

An kashe 'yan ta'adda sama da 40

Majiyoyi sun ce an kashe 'yan ta'adda fiye da 40 daga bangarorin biyu. Ya zuwa yanzu dai hukumar sojin Najeriya bata tabbatar da abin da ya faru ba.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin sunayen manyan yan siyasa 4 da tsohon gwamnan Ribas ya raba gari da su

Fadan da ake gwabzawa tsakanin kungiyoyin 'yan ta'addan biyu ya kara dagula sabbin kwararowar makamai.

Hakazalika, hakan ya kara yawan shigowar 'yan kungiyar ISIS ta Sahel don dafawa ISWAP a yankin tafkin Chadi domin sake kwato yankunanta daga hannun Boko Haram.

'Yan ta'adda sun mika wuya

Akalla mayakan kungiyar ta'addanci Boko Haram 1,250 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya tare da iyalansu a Arewa maso Gabas cikin kwanaki 7 da suka shige.

Rahoto ya nuna cewa hakan ba zai rasa alaka da artabun da suka yi da kungiyar ISWAP da basu ga maciji, lamarin da ya yi ajalin mayakan Boko Haram sama da 200.

Masani kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Magama, ya tattaro yadda ISWAP ta kai harin daukar fansa kan mayakan Boko Haram ranar 26 da 27 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.