An Shiga Jimamin Rashin Manoma 4 Da ’Yan Bindiga Suka Yiwa Kisan Gilla a Jihar Katsina

An Shiga Jimamin Rashin Manoma 4 Da ’Yan Bindiga Suka Yiwa Kisan Gilla a Jihar Katsina

  • Yanzu muke samun labarin yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka hallaka mutane a jihar Katsina da ke Arewa maso Yamma
  • An kuma sace wasu mutum takwas da aka bayyana an ceto uku daga cikinsu, kuma an jikkata wasu da dama
  • Jihohin Arewacin Najeriya na yawan fuskantar bazaranar tsaro da kuma mamayar 'yan bindiga da ke kisa da sace mutane don fansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Batsari, jihar Katsina - Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta ce an kashe manoma hudu tare da sace takwas bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Nahuta da ke karamar hukumar Batsari a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Abubakar Aliyu, wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya shaidawa TheCable cewa ‘yan bindigan sun dura kauyen ne da misalin karfe 2 na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yan fashi sun farmaki bankuna 2 a Ekiti, sun kashe mutum 3 tare da sace makudan kudade

Yadda 'yan bindiga suka kashe manoma a Katsina
An kashe manoma 4 a Katsina | Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Aliyu ya ce ‘yan bindigan sun far wa manoman ne a lokacin da suke girbin amfanin gonakinsu da ke bayan gari a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sace mutum 8 a Katsina

Ya ce an yi awon gaba da mutum takwas daga cikin manoman amma jami’an tsaro sun kubutar da mutane uku, inda ya ce ana kokarin ceto sauran biyar da ke hannun tsagerun, rahoton People Gazette.

A cewarsa:

"Eh, manoman dankali ne da ke girbin amfanin gonakinsu sai 'yan fashin suka kai musu hari suka bude musu wuta.
“An kashe hudu, uku sun jikkata, takwas kuma tafi da su a lokacin amma daga bisani an ceto uku.
“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na ranar Asabar.
"Jami'an tsaro suna aiki tukuru don ganin an ceto sauran mutanen."

Halin da ake ciki a Katsina

Tsawon shekaru, al’ummar Katsina da dama na fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga da ke kashewa tare da sace mutanen ba gaira babu dalili.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Mahara sun sace babban Sarki bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin hana garkuwar

A baya-bayan nan dai jami’an tsaro sun dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai wa al’ummar Zakka a karamar hukumar Safana ta jihar.

'Yan bindiga sun kama barawo

A wani abu da yayi kama da kura ke kiran kare maye, wata kungiyar 'yan bindiga sun cafke wani barawo a jihar Katsina.

PRNigeria ta tattaro cewa, barawon ya kware wurin cire rodi da karafuna daga kangon gine-gine a kauyukan jihar.

Barawon 'dan jari bolan ya shiga hannun 'yan bindigan dake sintiri a baburansu kamar yadda aka tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.