Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kama Barawo, Sun Mika Shi Hannun Jami'an Tsaro

Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kama Barawo, Sun Mika Shi Hannun Jami'an Tsaro

  • 'Yan bindiga a jihar Katsina sun kama barawo da ya kware a satar karafuna da rodi a kangwayen ginin jama'a
  • Tuni suka titsiye shi tare da saka shi a tsakiya da bindigu inda suka ilimantar da shi illolin sata da abubuwan da yake yi
  • Ba su yi kasa a guiwa ba, sun hanzarta gurfanar da shi a gaban shugaban al'umma amma daga bisani sun kai shi hannu hukuma don a hukunta shi

Katsina - A wani abu da yayi kama da kura ke kiran kare maye, wata kungiyar 'yan bindiga sun cafke wani barawo a jihar Katsina.

'Yan bindiga da barawo
Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kama Barawo, Sun Mika Shi Hannun Jami'an Tsaro. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

PRNigeria ta tattaro cewa, barawon ya kware wurin cire rodi da karafuna daga kangon gine-gine a kauyukan jihar.

Barawon 'dan jari bolan ya shiga hannun 'yan bindigan dake sintiri a baburansu kamar yadda aka tattaro.

Kara karanta wannan

Zaman Dubai Sai An Shirya: Bidiyon Wasu Karatan Maza Suna Aikin Wanke-Wanke Don Samun Na Kashewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani bidiyo da PRNigeria ta samo ya nuna 'yan bindigan sun kama barawon da karafunan da ya sata a cikin amalakensa sannan sun gurfanar da shi a gaban shugaban yankin.

Duk da ba za a iya tabbatar da ranar da lamarin ya faru ba daga bidiyon, an gano cewa 'yan bindigan sun ja kunnen barawon kan hatsarin dake tattare da sata.

Kamar yadda 'yan bindigan suka sanar:

"Baka san sata babban laifi bane? Ka ji dadi da ba mu mika ka hannun hukuma ba, da mun kaddamar maka da hukunci kan wannan laifin,"

'Yan ta'addan, wadanda a bidiyon suka bayyana rike da bindigogi, sun sanar da shugaban yankin da ya tabbatar an dauka mataki kan barawon kamar yadda doka ta tanada don hana jama'a sata.

PRNigeria ta tattaro cewa, daga bisani 'yan bindigan sun mika wanda ake zargin hannun hukuma domin a hakunta shi.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Babban Limami Da Wasu Mutum 3 A Jihar Borno

Zamfara: 'Yan Bindiga Sun Zuba Wadanda Suka Sace a Masallacin Juma'a a Gonakinsu

A wani labari na daban, Masallata 44 da 'yan bindiga suka sace daga Masallacin Juma'a a Zamfara suna gonakin 'yan bindigan inda suka zuba su suna musu noma, Daily Trust ta gano hakan.

Mazaunan yankin sun sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigan sun kira 'yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su tare da sanar musu cewa suna hannunsu amma suna aiki a gonakinsu na hatsi, har yanzu dai basu yi maganar kudin fansa ba.

"Gonakinmu na gero sun isa girbi kuma wadanda muka yi garkuwa da su suna mana aiki,"

Asali: Legit.ng

Online view pixel