Akwai Yiwuwar a Samu Sauki, Darajar Naira Ta Farfado Idan Aka Kwatanta da Dalar Amurka
- Darajar Naira takara farfadowa idan aka kwatanta da Dalar Amurka a kasuwannin canji a hukumance da kasuwar bayan fage
- A kasuwannin hada-hadar kudi, kwazon da darajar Naira ta yi a kan Dala ya tafi a jere na kwanaki biyu
- Habakar darajar Naira ta samu ne sakamakon saukin da aka samu na matsin lamba da raguwar bukata a kasuwannin saye da sayarwa
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Najeriya - Darajar Naira ta samu karuwa idan aka kwatanta da Dalar Amurka a kasuwannin musayar kudi a karshen makon nan.
Bayanan da aka samu daga FMDQ sun nuna cewa darajar Naira ta koma N889.86/$1 a ranar Juma’a, 15 ga Disamba, 2023.
Wannan dai karin daraja ne na 1.3% ko kuma N11.55 idan aka kwatanta da Dalar Amurka; fiye da na ranar Alhamis N901.41/$1.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karuwar makon da ya gabata
Haka kuma wani gagarumin ci gaba ne da 23.51% ko kuma N209.19 daga faduwar da Naira ta yi; N1,099.05/$ ya zuwa ranar Juma’ar da ta gabata, 8 ga watan Disamba.
Habakar darajar Naira dai ya biyo bayan karancin bukatar musayar kudaden kasashen waje (FX) a kasuwanni.
Bayanai sun nuna cewa farashin da aka samu na cinikayya ya ragu da 71.70% ko kuma Dala miliyan 105.54 zuwa Dala miliyan 41.66 daga Dala miliyan 147.20 da aka ambato a ranar Alhamis.
Farashin Naira da Dala a kasuwar bayan fage
Hakazalika, Naira ta inganta idan aka kwatanta da Dala a kasuwannin bayan fage guda biyu - Peer-to-Peer (P2P) da kuma ta asalin bayan fage.
A hannun 'yan P2P, Naira ta samu karuwar N3, inda ta kai N1,207/$1 idan aka kwatanta da N1,210/$ da aka gani a baya.
Hakazalika, kudin na Najeriya ya kara inganta darajarsa idan aka kwatanta da Dala a kasuwan bai daya a ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba, 2023.
A cewar rahoto, Naira ta kara N15 inda ta koma N1,235/$1, sabanin farashin da ya kasance a ranar da ya gabata na N1,250/$1.
Naira ta gama zabure-zabure, ta fadi a baya
A wani labarin, kudin Najeriya na Naira ya na cigaba da gangara a sahun kudin duniya, yanzu ana sayen Dala a kan fiye da N1,000.
Rahoton da The Cable ta fitar a tsakiyar makon nan ya ce sai mutum ya bada N1,120 kafin ya iya samun duk Dalar Amurka guda.
Fadin da darajar Naira ta yi a ranar Talata ya kai 9.27% ko kuma a ce kudin Najeriyan ya rasa N95 na kimarsa a cikin sa’o’i 24.
Asali: Legit.ng