Buhari Ya Cika Shekaru 81 a Duniya, Tinubu Ya Tura Masa Sakon Taya Murna Mai Ban Mamaki

Buhari Ya Cika Shekaru 81 a Duniya, Tinubu Ya Tura Masa Sakon Taya Murna Mai Ban Mamaki

  • Shugaba Tinubu ya bi sahun jiga-jigan kasar nan wajen tura sakon taya murnar cika shekaru 81 ga Buhari
  • Buhari ya yi murnar cika shekaru 81 a duniya, wannan ne karo na farko cikin shekaru takwas da ya yi bikin ba a Villa ba
  • Tinubu ya tuna da wasu halayen Buhari na kirki, yace kaddara ce ke samar da shugaba irin Buhari a duniya

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya mika sakon taya murnar cikan shekaru 81 ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A yau ne rahotanni suke bayyana cewa, tsohon shugaban ya cika shekaru 81 a duniya, ana ta taya shi murna.

Kara karanta wannan

Kaddara Ce Ta Kawo Buhari Mulkin Najeriya, Tinubu Ya Magantu Kan Salon Mulkin Tsohon Shugaban Kasar

Buhari ya cika shekaru 81 a duniya, Tinubu ya yi murna
Tinubu ya taya Buhari murnar cika shekaru 81 a duniya | Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Buhari ya cika shekaru 81, murnar farko bayan kammala mulki

Idan baku manta ba, a watan Mayun wannan shekarar mai karewa ne Buhari ya mika mulki ga Tinubu bayan shafe shekaru takwas yana jan ragamar kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ne karon farko cikin shekaru takwas da Buhari zai yi bikin shekara ba a cikin fadar shugaban kasa ba.

Kamar yadda aka saba, wannan karon ma ana ta turawa shugaban sakwannin murnar cika shekara.

Ba a bar shugaba Tinubu a baya ba, ya mika sakonsa ta hannun hadiminsa a fannin yada labarai.

Kaddara ke samar da shugaba irin Buhari, Tinubu

Mai magana da yawun shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fadi a shafinsa na Twitter cewa:

“Shugaba Buhari…ya sadaukar da rayuwarsa wajen yiwa kasa hidima, har ma ya samu kansa a magarkama saboda kishin kasa da yi wa kasarmu hidima.

Kara karanta wannan

Tinubu: Mutum 2 da za su taimakawa gwamnatinmu wajen samun nasara a Najeriya

"Samuwar shugabanni irin na babban abokina, Buhari, kaddara ce kadai ke samar dasu, mutum ne mai cikakken togewa da mutunci mara sarrafuwa, idan yace a'a, to yana nufin a'a."

Lokacin da Buhari ya cika shekaru 80

A baya kun ji cewa, Muhammadu Buhari wanda ke bikin cika shekaru 80 a yau Asabar, 17 ga watan Disamba ya fuskanci zarge-zarge daga magautansa.

Koda dai shugaba Buhari ya hau mulki da niyan kawo chanji, mutane da dana suna ganin ya gaza cika alkawaran da ya dauka yayin yakin neman zabensa bayan ya lashe zabe a 2015.

Joe Ibokwe, wani dan kashenin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, ya lissafa wasu zarge-zargen da aka yiwa shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel