Masoya Sun Yi Aure Bayan Shekaru 29 Tare da Haihuwar Manyan Yara, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Masoya Sun Yi Aure Bayan Shekaru 29 Tare da Haihuwar Manyan Yara, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Wata budurwa yar Najeriya wacce iyayenta suna yi aure bayan shekaru 29 a tare ta yada bidiyon shagalin bikinsu
  • Kawayen budurwar sun halarci taron domin taya ma'auratan murna a yayin da suka cimma dadadden mafarkinsu
  • Daga cikin wadanda suka yi martani kan bidiyon tsoffin ma'auratan harda mutanen da suka yi al'ajabin dalilinsu na dadewa kafin su yi aure

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin yada bidiyon auren iyayenta, wadanda suka shiga daga ciki bayan shekaru 29.

Tuni ma'auratan suka mallaki yara da suka girma a daidai lokacin da suka yi aure a hukumance.

Masoya sun yi aure bayan shekaru 29 tare
Masoya Sun Yi Aure Bayan Shekaru 29 Tare da Haihuwar Manyan Yara, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce Hoto: @misttyceleb1
Asali: TikTok

Tsoffin ma'aurata sun taya kansu murna

Gaba daya abokan yaran sun yi wani sanannen wasa da aka yi na wacece amarya don nunawa duniya ainahin amaryar.

Kara karanta wannan

"Shugaba a shekaru 20": Yar Najeriya ta yi tattalin kudinta da kyau, ta gina hadadden gidan dinki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashiyar (@misttyceleb1) wacce ta yada bidiyon ta taya iyayenta murna. Mutane da dama sun taya ma'auratan murna, sannan wasu sun yi mamakin dalilinsu na jira na tsawon lokaci.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon ma'aurata da suka kwana biyu

LK markie ta ce:

"An kunsa mata ciki tana yar yarinya yanzu ta yi aure a hukumance."

Oluwatobiloba Godwin ya ce:

"Wannan ya yi kyau. Allah ubangiji ya ci gaba da sanya albarka a aurensu."

de Frank ya ce:

"Wacce ta ce abincin ne ya kawo ta tana shiga mun ido."

Mabel’stouch cosmetics ta ce:

"Ina tayaki murna iya mistura na yi matukar ji maki dadi."

Sadiya ta ce:

"Awwn na taya su murna ta yi kyau matuka karin rayuwar farin ciki a tare."

ireoluwa ta ce:

Kara karanta wannan

Budurwa za ta yi wuff da abokin saurayinta, ta saki zafafan hotunan kafin aure

"Ina taya su murna. Mama na cikin tsantsar farin ciki."

user2689506725640 ya ce:

"Diyarta kawar amarya."

Quin Belbon ta ce:

"Amarya na cikin tsantsar farin ciki."

Budurwa za ta yi wuff da abokin saurayinta

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiya yar Najeriya ta saki katin gayyata zuwa wajen daurin aurenta.

Budurwar wacce ta kuma saki hotunan kafin aurensu, ta ce angon nata abokin tsohon saurayinta ne.

Ta ce ya nemi ta aure shi lokacin da suke tsaka da soyayya da abokinsa, kuma ta amince masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng