An Kama Wani Mutum Bayan Ya Ziyarci Surukansa Ba Tare da Sadaki ba, Sun Dafa Abinci da Komai Na Biki

An Kama Wani Mutum Bayan Ya Ziyarci Surukansa Ba Tare da Sadaki ba, Sun Dafa Abinci da Komai Na Biki

  • An kama wani dattijo shekaru 60 kan kin kai wa surukansa sadakin auren diyarsu
  • Ya bukaci dangin amaryar da su biya kudaden da za a kashe na bikin da nufin biyansu amma ya saba yarjejeniyar
  • Dattijon ya ba da hakuri sannan ya yi alkawarin biyansu abun da suka kashe a bikin da aka fasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani al'amari ya afku a yankin Bukwo, inda wani mutum mai suna Samuel Maikut, ya je gidan surukansa ba tare da kudin sadakin da ake sa ran zai kawo ba, lamarin da ya dimauta dangin amaryar tare da fusata su.

Kamar yadda Ugandan Monitor ta rahoto, Maikut ya fada ma dangin cewa yana so ya auri diyarsu a aure irin na gargajiya sannan ya bukaci da su yi komai na shagalin bikin.

Kara karanta wannan

"Yan sanda sun yi garkuwa da ni, sun karbi Naira miliyan 1 kudin fansa", cewar Mr Soyemi

Yan sanda sun kama mutumin da ya saba alkawarin surukansa
An Kama Wani Mutum Bayan Ya Ziyarci Surukansa Ba Tare da Sadaki ba, Ya Amsa Laifinsa Hoto: Ugandan Monitor/UGC
Asali: UGC

Iyayen amaryar sun kashe makudan kudi da ya kai naira miliyan 1.2, kan shirye-shiryen bikin, suna sa ran Maikut ya zo da shanu hudu da akuya uku, kamar yadda suka kulla yarjejeniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, da ranar da ake jira ta zo, Maikut ya iso hannu goma, kafa goma yana mai saba yarjejeniyar da suka kulla.

Abun da ya fi komai muni, Maikut ya yi lattin zuwa wajen, ya zo mintuna 20 bayan lokacin da aka tsayar 5:00 na yamma. Lattin zuwansa da rashin kawo kudin sadaki ya kara tabarbarar da lamarin.

Yan uwan amaryar, sun fusata, suka tambayi Maikut kan dalilinsa na saba alkawarinsa, amma ya gaza bayar da gamsasshiyar amsa.

Yayin da lamarin ya koma tashin hankali, sai aka kira hukumomin kauyen, wanda ya kai ga yan sanda sun kama Maikut.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

Daga bisani, dattijon mai shekaru 60 ya bayar da hakuri kan lamarin sannan ya yi alkawarin mayarwa iyayen amaryar kudaden da suka rasa kan bikin da aka fasa.

Budurwa zata yi wuff da abokin saurayinta

A wani labarin, mun ji cewa Favour Okenwa, wata matashiya yar Najeriya, ta sanar da labarin aurenta mai zuwa kuma lamanta sun haddasa cece-kuce tsakanin mutane.

A wata wallafa da ta yi a dandalin Facebook a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, matashiyar ta mato kan angon nata sannan ta saki katin gayyata zuwa waje daurin auren nasu dauke da hotunan kafin aurensu guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng