Innalillahi: Mahaifiyar Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Haifan, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Innalillahi: Mahaifiyar Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Haifan, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Da yammacin jiya Juma'a ce Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdurrazak Yahaya Haifan
  • Marigayiyar ta rasu ne da yammacin Juma'ar ce 15 ga watan Disamba a birnin Tarayyar Najeriya, Abuja
  • An sanar da sallar jana'izar marigayiyar yau Asabar da misalin karfe 10:00 na safe a Gwagwalada da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mahaifiyar babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abdulrazak Yahaya Haifan ta rasu.

Marigayiyar ta rasu ne da yammacin jiya Juma'a 15 ga watan Disamba a birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

Sheikh Haifan ya rasa mahaifiyarsa da yammacin jiya Juma'a
Marigayiyar ta rasu ne da yammacin jiya Juma'a a Abuja. Hoto: Abdurrazaq Yahaya Haifan (Facebook).
Asali: Facebook

Yaushe za a yi sallar jana'izar marigayiyar?

Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi jana'izar marigayiyar ce a yau Asabar 16 ga watan Disamba da misalin karfe 10:00 na safe a Gwagwalada da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Manyan malamai sun dira hedkwatar tsaro ta kasa yayin da CDS ya dauki sabon alkawari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Haifan ya kasance babban malamin addinin Musulunci a Najeriya da ya ke ba da gudunmawa a ilmantar da mutane addini.

Bangaren yada labarai ta JIBWIS reshen Abuja ta bayyana cewa marigayiwar ta rasu ne yayin da malamin ke karatun littafin da ya daba yi duk ranar Juma'a bayan sallar Mangariba.

Farfesa Isa Ali ya samu halartar jana'izar

Manyan mutane sun samu halartar jana'izar da aka gudanar a Masallacin Zango dake Gwagwalada a Abuja.

Daga cikinsu akwai shararren malamin addinin Musulunci kuma tsohon Ministran Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.

Wannan na zuwa watanni kadan bayan rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu a Birnin Kebbi da ke jihar Kebbi a ranar 6 ga watan Satumba.

Mutuwar Giro ta girgiza al'ummar Musulmai inda su ka bayyana cewa ba za a iya misalta gudunmawar da ya bayar ba.

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojoji sun tarwatsa mafakar hatsabiban yan bindiga, sun kashe wasu a jihohin arewa 2

Allah ya karbi rayuwar babban malamin addinin Musulunci

A wani labarin, Babban limamin masallacin Izala da ke unguwar Abuja a birnin Gombe ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin, Imam Sa'idu Abubakar rasu ne a ranar 17 ga watan Nuwamba bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya tura sakon jaje ga iyalan mamacin inda ya yi addu'ar ubangiji ya masa rahama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.