Matar shahararren dan wasan kwaikwayo 'Samanja' ta rasu

Matar shahararren dan wasan kwaikwayo 'Samanja' ta rasu

Uwar gidan fittacen dan wasan kwaikwayon nan Usman Baba Pategi da aka fi sani da 'Samanja"ta rasu.

Hajiya Maryam Usman Baba ta rasu ne a ranar Laraba a asibitin kwararu na Barau Dikko da ke garin Kaduna tana da shekaru 43 a duniya kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Daya daga cikin 'ya'yan Samanja, Abubakar Usman ya tabbatar da rasuwar mahaifiyarsa inda ya ce ta dade tana fama da ciwon suga da hawan jini na fiye da shekara daya.

DUBA WANNAN: Zaben Gwamna: APC tayi martani a kan nasarar da Adeleke ya yi a kotu

Matar shararen dan wasan kwaikwayo 'Samanja' ta rasu
Matar shararen dan wasan kwaikwayo 'Samanja' ta rasu
Asali: Twitter

A cewarsa, "An kwantar da ita a asibitin kwararu na Barau Dikko na sama da makonni uku kafin ta rasu a ranar Laraba misalin karfe 3.30 na yamma."

Ta rasu ta bar mijinta, mahaifinta da yayar ta.

Tuni dai anyi jana'izarta a makabartar musulmi na Kabala Doki kamar yadda bisa koyarwan addinin musulunci.

Samanja ya shahara ne sakamakon wasan kwaikwayo na tarihi mai suna 'Samanja' da ya fito a ciki da ake haskawa a gidan talabijin na kasa NTA a a shekarun baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164