Shoprite Za Su Yi Gaba, Kamfanoni 22 Na Hanyar Shigowa Najeriya Da Kudi Domin Kasuwanci
- Hukumar NIPC ta iya yin zama da wasu kamfanonin kasashen waje wadanda su ke son yin kasuwanci
- Wadannan kamfanoni za su nemi cin moriyar yawan mutanen Najeriya domin ganin sun samu kudi
- Shugabar NIPC ta ce ana kokari wajen ganin yadda za a kwadaito ‘yan kasuwa cikin jihohin Najeriya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Hukumar NIPC mai alhakin jawo masu hannun jari ta sanar da cewa tana kokarin hada kai da wasu kamfanonin kasar Jamus.
A makon nan Daily Trust ta rahoto shugabar NIPC, Aisha Rimi ta na cewa akwai alakar kasuwancin £3bn tsakanin Najeriya da Jamus.
NIPC za ta kawo kamfanonin Jamus
Aisha Rimi tayi wannan bayani ne a sa’ilin da ta ke tattaunawa da kamfanonin waje fiye da 22 da su ke son yin kasuwanci a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadannan kamfanoni sun fito ne daga Jamus da sauran kasahen nahiyar Turai.
A lokacin da kamfanoni irinsu GSK, P & G da Shoprite su ke son barin kasar, wasu kuma sun nuna sha’awar su kawo kudinsu Najeriya.
Alakar Najeriya da kamfanonin waje
Ministan harkokin kasar waje, Yusuf M. Tuggar ya ce mafi yawan kasashen ketaren da ke zuwa kasuwanci Najeriya daga Turai suka fito.
Ambasada Yusuf Tuggar yake cewa Najeriya ta samu $806.33m daga fita da kaya zuwa kasashen Jamus a shekarar 2022 da ta wuce.
Ministan ya ce kasashen Turai sun kashe makudan kudi wajen kasuwanci da kasar nan.
Rahoton ya ce Rimi ta samu damar yin zama da jihohi domin fito da inda su kayi fice ta yadda kamfanoni za su domin zuba hannun jari.
Kamfanoni za su taimakawa gwamnati
"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya
Shugaban tawagar Jamusawa a Najeriya, Micheal Schmidt ya ce kamfanoni sama da 22 sun ziyarci kasar nan domin ayi harka ta arziki.
Kamfanonin wajen za su zo da kudi su yi kasuwanci wanda masana suna ganin zai samar da ayyukan yi ya kawowa kasar kudin shiga.
Sanusi II ya soki gwamnatin Buhari
Kwanakin baya aka ji labarin yadda Khalifa Muhammadu Sanusi II ya soki shekaru 8 na mulkin Muhammadu Buhari da aka yi a Najeriya.
Masana tattalin arziki irinsu Sanusi II sun soki hanyar da aka bi wajen buga kudi a CBN, ana zargin adadin ya doshi Naira tiriliyan 22.7.
Asali: Legit.ng