Karancin Kudi Ya Tilasta Masu Sana'ar POS Kara Kudin da Suke Caja Zuwa N400 Kan N10,000

Karancin Kudi Ya Tilasta Masu Sana'ar POS Kara Kudin da Suke Caja Zuwa N400 Kan N10,000

  • Masu sana'ar PoS sun kara kudin da suke caji da kaso 100 saboda karancin kudi da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya
  • Wasu masu PoS sun yi zargin cewa ma'aikatan banki su kan bukaci 10% a kan kowani kudi da aka cire
  • A kwanan nan ne Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa kudaden da ke zagaye a gari sun zarce na lokacin da ake sake fasalin naira

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ana ci gaba da fama da karancin kudi a fadin Najeriya makonni biyu tun bayan da Babban Bankin Najeriya ya tabbatar wa al'ummar kasar cewa akwai isassun kudi da zai isa gudanar da harkokin kasuwanci.

Karancin kudin da ake fama da shi a yanzu ya sa masu sana'ar PoS sun kara kudin caji da suke karba da kaso dari, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Kasafin 2024: Minista na rokon majalisa ta karawa ma'aikatarsa Naira biliyan 250

Masu PoS ta kara caji
Karancin Kudi Ya Tilasta Masu Sana'ar POS Kara Kudin da Suke Caja Zuwa N400 Kan N10,000 Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: UGC

Masu PoS suna karban N400 yayin cire N10,000

Ci gaban ya kuma sa bankuna tsara fitar kudi da takaita cire kudade a fadin ATM da sauran wuraren cire kudi a fadin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya kara tabarbarewa a wasu jihohi, musamman a Lagas, inda yawancin na'urorin ATM suka zama ba kudi ko dogon layi na masu cire kudi.

Masu PoS, wadanda sune mafitan karshe da yan Najeriya ke da shi na samun kudi sun kara caji zuwa N400 kan kowani N10,000 da mutum zai cire maimakon N200 da suke caji a baya.

Ma’aikatan banki suna karbar cakwado yayin da CBN ya bayyana adadin kudin da ke zagaye

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa masu PoS sun yi zargin cewa ma'aikatan banki kan bukaci N10,000 kan kowani N100,000 da za a cire.

Bincike ya nuna cewa bankuna sun takaita cire kudi a kanta zuwa N20,000 da kuma N50,000.

Kara karanta wannan

Abin da ya jawo ake wahalar kudi a yau – A karshe bankin CBN ya yi karin bayani

A fadin ATM kuma, bankuna sun takaita cire kudi zuwa N5,000 maimakon N100,000 na baya.

Babban bankin Najeriya ya tabbatar wa‘yan Najeriya a ranar Laraba, 13, 2023, cewa akwai isassun kudade da ke yawo a kasar, tare da dora alhakin karancin kudin kan masu boye shi.

Legit Hausa ta tuntubi wata mai PoS da ta nemi a sakaya sunanta inda ta tabbatar da lallai ba son ransu bane yasa suka kara kudin cajin, tana mai cewa:

“Haka ne kudin caji ya karu kamar mu nan muna karbar N300 ne kan kowani N10,000 kuma ba wai haka kawai muka kara ba, cajin da bankuna suke yi mana ne ya karu.
“Sana’ar PoS dinnan kawai dai ya fi zama haka kawai ne amma ba wani riba bane a ciki, mu kadai muka san gwagwarmayar da muke yi kafin mu samo kudin ma. Kin ga a da N50 muke caji a abun da ya yi kasa daN5,000 yanzu ya koma N100.”

Kara karanta wannan

Gagaruman abubuwa 3 da za su faru a 2024, malamin addini ya yi hasashe

Jabun kudi na yawo, CBN

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa yayin da ake fama da karancin kudi a Najeriya, Babban Bankin kasar ta gargadi yan Najeriya a kan jabun kudade da ke yawo.

Babban bankin kasar ya yi gargadin ne a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba mai taken "ku yi hattara da jabun kudi da ke yawo".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng