Wata sabuwa: Keyamo Ya Bi Sahun Tinubu, Ya Kori Daraktoci 33 Na Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama
- An raba wasu manyan jami'an gwamnati da ministan Buhari ya nada da aikinsu
- Gwamnatin Shugaban kasa Tinubu ta sallami shugabannin hukumar sufurin jiragen sama da Sanata Hadi Sirika, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya nada
- A halin da ake ciki, masana harkokin sufurin jiragen sama wadanda suka tabbatar da ci gaban sun kare matakin da gwamnati mai ci ta dauka
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi umurnin sallamar daraktoci 33 a karkashin ma'aikatarsa.
Dalilin da ya sa Keyamo ya kori dukkan daraktoci a ma'aikatar sufurin jiragen sama
Masana harkokin sufurin jiragen sama sun tabbatar wa manema labarai hakan a Abuja, a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnati ma ta tabbatar da ci gaban a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun Keyamo, Odutayo Oluseyi, ranar Alhamis a Abuja.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maanan sun bayyana ci gaban a matsayin "tsaftacewa da sauya nade-naden mukamai na kurarren lokaci” da gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi a lokacin da Sanata Hadi Sirika yake ministan sufurin jiragen sama.
A ranar 23 ga watan Mayun 2023, mako guda kafin karewar gwamnatin Buhari, Sirika ya nada daraktoci 33 sannan ya nada sabbin manajan darakta a hukumomin FAAN da NAMA.
Ya kuma samar da daraktocin da babu su a dukkan hukumomin.
Sai dai kuma watanni shida bayan nan, an tsige gaba daya mutanen da ya nada ba tare da saninsu ba, a wani gagarumin yamutsi da ya zo wa su kansu wadanda aka sallama a bazata a hukumomin sufurin jiragen saman, rahoton The Cable.
Kasa da awa 24 bayan Tinubu ya kori shugabannin hukumomi, ya sake korar daraktocin da Buhari ya nada
Manyan jami'an gwamnati 9 da aka tsige
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa har yanzu Shugaban kasa Bola Tinubu bai gama tsige manyan jami'an gwamnati tare da nada sabbi ba watanni shida bayan ya karbi ragamar shugabanci.
Gwamnatin da ta shude ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta nada wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin da abun ya shafa.
Asali: Legit.ng