Rikicin Rivers: Jerin Kwamishinoni 4 da Suka Ajiye Aiki Saboda Wike, Suka Juya Wa Fubara Baya

Rikicin Rivers: Jerin Kwamishinoni 4 da Suka Ajiye Aiki Saboda Wike, Suka Juya Wa Fubara Baya

  • Rikicin siyasar da ke tsakanin Nyesom Wike da magajin sa ba zai kare don yanzu ba yayin da aka samu karin kwamishinoni da suka juya wa Gwamna Fubara baya
  • Hakan na zuwa bayan da kwamishinan ayyuka, Dr George-Kelly Alabo, da takwararsa Mrs. Inime Chinwenwo-Aguma suka yi murabus
  • Aguma ta ba da dalilin yin murabus da cewa "wasu dalilai da suka shafi rayuwata," yayin da Alabo ya ce "amfani da hankali"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Rivers - Har yanzu dai rikicin siyasa na ci gaba da ruruwa a jihar Rivers, inda a kwanan nan lamari yayi tsamari yayin da kwamishinoni ke ajiye ayyukansu.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito a yammacin ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba, kwamishinoni hudu ne suka ajiye aikin su saboda Wike.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kwamishinoni huɗu sun yi murabus daga muƙamansu a jihar PDP, sun faɗi dalili

Kwamishinonin Rivers 4 sun ajiye aiki
Rikicin Wike da Fubara ya kara tsamari, kwamishinonin Rivers 4 sun ajiye aiki a tare. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara, @kc_journalist
Asali: Facebook

Kwanishinan ayyuka na mujsamman, Emeka Woke, da kwamishinan Kudi, Isaac Kamalu su ka yi murabus daga mukarraban Gwamna Fubara, Premimum Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka yi murabus sun bayyana cewa akwai dangantaka mai karfi tsakaninsu da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Kamalu shi ne kwamishina na hudu da ya yi murabus wanda ya bi bayan Zacchaeus Adangor, Dax Kelly da Inime Aguma.

Wasu karin kwamishinoni 2 sun yi murabus ana tsaka da rikicin Wike da Fubara

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa kwamishinan ayyuka wanda dan a mutun tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike ne, Dr Gearge-Kelly Alabo ya yi murabus.

Haka zalika kwamishiniyar ayyukan jama'a walwala, Mrs Inime Chinwenwo-Aguma ta yi murabus, Legit ta ruwaito.

Sun yi murabus din ne a ranar 14 ga watan Disamba a wata wasika da suka aika wa Gwamna Siminalayi Fubara ta hannun sakataren gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

"Zamani ya canza" Shugaban JAMB ya faɗa wa ɗalibai yadda zasu samu aiki bayan gama digiri a Najeriya

Rikicin Wike da Fubara: Antoni Janar na jihar Rivers ya yi murabus

Haka zalika, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa Zacchaeus Adangor, antoni janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Rivers ya yi murabus daga kujerarsa.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito a ranar Alhamis 14 ga watan Disamba, Adangor ya aika takardar ajiye aikin sa kai tsaye ga Gwamna Siminalayi Fubara.

Gwamna Fubara ya fadi dalilin rushe ginin majalisar dokokin jihar Rivers

A wani labarin kuma, Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta rushe gininin majalisar dokokin jihar ne don gina sabuwa biyo bayan gobara da ta lalata ta.

Vanguard ta ruwaito sanarwar na cewa Fubara ya amince 'yan majalisun jihar su yi amfani da wani sashe da ke cikin fadar gwamnatin jihar don gudanar da zaman su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.