An Ga Tashin Hankali Bayan Gini Ya Ruguje Kan Mata Da Jaririnta Mai Kwanaki 9, Mijin Ya Shiga Yanayi

An Ga Tashin Hankali Bayan Gini Ya Ruguje Kan Mata Da Jaririnta Mai Kwanaki 9, Mijin Ya Shiga Yanayi

  • Wani ni ya ruguje kan wata mata da jaririnta mai kwanaki tara kacal a duniya a birnin Akure da ke jihar Ondo
  • Lamarin ya faru ne a jiya Laraba 13 ga watan Disamba a kan hanyar Ayedun kusa da asibitin Egbe a birnin Akure
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Funmilayo Odunlami ba ta mai da martani ba kan wannan lamari da ya faru

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Jimami yayin da wata mata da jariri dan kwana tara kacal a duniya su ka rasu bayan gini ya ruguje a kansu.

Lamarin ya faru ne da safiyar jiya Laraba 13 ga watan Disamba a birnin Akure da ke jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Allah Sarki: Mahara sun sace babban Sarki bayan hallaka hadiminsa da ya yi kokarin hana garkuwar

Gini ya ruguje kan wata mata da jaririnta dan kwana 9 a jihar Ondo
Lamarin ya faru ne a Akure da ke jihar Ondo a jiya Laraba. Hoto: Ondo Police Command.
Asali: Facebook

Mene mutane ke cewa kan lamarin?

Har ila yau, dan uwan jaririn da kuma kakarsu sun tsallake rijiya da baya yayin aka kawo musu dauki sai dai sun samu raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Ayedun kusa da asibitin Egbe a birnin Akure inda matar ta makale da jaririn har su ka mutu.

Wani shaidan gani da ido da ya bukaci a sakaye sunanshi ya bayyana mutuwar da abin takaici.

Ya ce:

"Wannan mutuwar ta tayar mana da hankali inda wani babban dam na ruwa ya fado kan ginin da ya yi ajalin mutanen.
"Kwankeren da ke rike da dam din ruwan ya na da karfi kawai dai tsautsayi ne, a ranar Talata 12 ga watan Disamba aka yi bikin sunan jaririn."

Mene 'yan sanda su ka ce?

Kara karanta wannan

Daliban Firamare 18 sun kwana a asibiti kan cin abinci da gwamnati ke bayar wa, an fadi dalili

Ya ce karar faduwar ginin ne ya jawo hankalin mutane a wurin amma ba su iya yin wani abu ba ganin yadda ginin ya danne su, cewar Leadership.

Ya kara da cewa zuwan mutane ma sun samu sun riga sun mutu, don haka babu abin da za su iya yi, jami'an tsaro sun kwashe su zuwa asibiti.

Daga daga cikin wadanda ke zaune a gidan ya bayyana cewa mijin marigayiyar ya fita kafin abin ya faru.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Funmilayo Odunlami ba ta mai da martani ba sai dai wani babban dan sanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Tinubu ya shiga tsakani a rikicin Ondo

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya sake sanya baki a rikicin siyasar jihar Ondo.

Wannan shi ne karo na biyu da shugaban ke kokarin kawo karshen rikicin da ke kara ruruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.