Gwamnan Arewa Ya Nada Tsohon Soja a Matsayin Shugaban Hukumar Hisbah, Ya Fadi Dalili
- Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya yi sabbin nade-nade a hukumomi da dama da su ka hada da Hisbah
- Radda ya nada Ahmad Daku a matsayin shugaban Hisbah wanda tsohon gwamnan jihohin Kano da Sokoto ne a mukin soja
- Wannan na kunshe na a cikin wata sanarwa da Ibrahim Kaula, daraktan yada labaran gwamna ya fitar a jiya Laraba 13 ga watan Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina – Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya nada Ahmad Daku a matsayin shugaban Hukumar Hisbah a jihar.
Daku shi ne tsohon gwamnan jihohin Kano da Sokoto a mulkin soja kafin ya yi ritaya daga aiki.
Waye ne sabon shugaban Hisbah?
Wannan na kunshe na a cikin wata sanarwa da Ibrahim Kaula, daraktan yada labaran gwamna ya fitar a jiya Laraba 13 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kaula ya ce Radda ya kuma amince da nadin shugabannin wasu hukumomi na daban a jihar, cewar TheCable.
Sabon shugaban Hisbah ya mulki jihar Kano ce a shekarar 1985 zuwa 1987 yayin da ya mulki Sokoto a shekarar 1987 zuwa 1990.
A shekarar 2022 ya jagoranci hukumar Alhazai ta jihar inda kuma ya nemi takarar gwaman a 2003 inda Umaru Yar’adua ya kayar da shi.
Wasu mukamai kuma Radda ya nada?
Gwamnan ya kuma nada Aminu Abubakar a matsayin kwamandan hukumar Hisbah yayin da Kamal Alti da Iliya Imam da Sirajo Lawal za su kasance mambobi.
Har ila yau, Gwamna Radda ya nada shugabannin hukumomin Zakkah da Wakafi da Hukumar kula da kudade da na kananan hukumomi da sauransu.
Ahmed Filin-Samji shi ne shugaban hukumar Zakkah da Wakafi da sauran lamuran da su ka shafi wannan layin, cewar Daily Nigerian.
Tinubu ya sallami shugabannin hukumomin FAAN, NAMA
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya kori shugabannin hukumomin FAAN da NAMA da ke karkashin ma'aikatar kula da jiragen sama.
Tinubu ya sallami Kabir Mohammed a matsayin shugaban FAAN tare da maye gurbinsa da Olabunmi Kuku.
Har ila yau, ya kori Tayyib Odunowo a matsayin shugaban NAMA tare da maye gurbinsa da Umar Farouk.
Asali: Legit.ng