Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Babbar Kungiya a Abuja a Bayan Gidan Tinubu
- Kakakin rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta mayar da martani kan harin da wasu ƴan bindiga suka kai a Abuja
- Adeh ta bayyana cewa iyalansa ba su kai rahoton sace John Emmanuel a ofishinsu ba, don haka ƴan sanda ba su ɗauki mataki ba
- A halin da ake ciki, matar mutumin ta bayyana cewa masu garkuwa da mutanen suna neman naira miliyan 15 a matsayin kuɗin fansa kafin shugaban jaridar ya samu ƴancinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An yi garkuwa da shugaban ƙungiyar dillalan jaridu ta birnin tarayya Abuja, John Emmanuel.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da Mista Emmanuel ne a hanyarsa ta komawa gida, a unguwar Giri da ke babban birnin tarayya Abuja a daren ranar Talata, 12 ga watan Disamba.
Masu garkuwa da mutanen sun buƙaci iyalansa da su biya Naira miliyan 15 a matsayin kudin fansa, domin ya shaƙi iskar ƴanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar mutumin, Mrs Uche Emmanuel, a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, a wata hira, ta tabbatar da sace mijinta yayin da ta kuma bayyana cewa waɗanda suka sace shi sun kira suna neman kuɗin fansa domin ya samu ƴanci.
A kalamanta:
"Eh, an sace mijina a Giri ranar Talata da misalin ƙarfe 8:00 na dare. Yana cikin motar tasi ne a hanyarsa ta komawa gida, abin takaici, motar ta miyagu ce, kuma suna neman Naira miliyan 15 kafin su sake shi."
Ƴan sanda sun mayar da martani
A halin da ake ciki, rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce har yanzu ba a kai rahoton lamarin ga ƴan sanda domin su ɗauki mataki ba.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, sai ta kada baki ta ce:
"Har yanzu babu rahoton wannan lamarin da aka kai a ofisoshin mu. Wataƙila iyalan ba su tuntuɓe mu ko kai rahoto gare mu (ƴan sanda) ba tukunna, ba za mu iya sanin abin da ba a sanar da mu ba."
Ƴan Bindiga Sun Halaka Sojoji a Rivers
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka sojoji huɗu a yayin wani kwanton ɓauna a jihar Rivers.
Ƴan bindigan dai sun yi kwanton ɓauna ne yayin da sojojin ke raka wani ayarin motocin wani kamfanin mai zuwa jihar Bayelsa.
Asali: Legit.ng