Gwamnatin Tarayya Ta Bada Dalilin Dakatar da Albashin Ma’aikata 686 Bayan Bincike

Gwamnatin Tarayya Ta Bada Dalilin Dakatar da Albashin Ma’aikata 686 Bayan Bincike

  • Gwamnatin tarayya ta tsaida albashin wasu ma’aikatanta biyo bayan binciken da aka gudanar a watan Oktoba
  • Wasu sun gyara kura-kuran da aka samu a bayanansu, daga baya za su cigaba da karbar albashi a karshen wata
  • Amma an samu wasu da ake ikirarin ma’aikata ne da ba su halarci tantacewar da aka yi ba, an cire su daga IPPIS

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A kokarin da ake yi na tsabtace masu karbar albashi da korar ma’aikatan bogi, gwamnati ta dakatar da albashin wasu ma’aikata.

A rahoton da aka samu daga Leadership, an ji cewa gwamnatin tarayya ta bada sanarwar tsaida albashin ma’aikata a sakamakon bincike.

TINUBU
Shugaban kasa ya sa a binciki ma'aikata Hoto: @Dolusegun16
Asali: Twitter

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr. Folasade Yemi-Esan ta sanar da haka a wani jawabi da ta fitar a ranar Larabar a garin Abuja.

Kara karanta wannan

IPPIS: Shugaba Tinubu ya sauya matakin da Buhari ya ɗauka kan jami'o'i da wasu manyan makarantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin ya fito ne ta bakin Darektan sadarwa na ma’aikatar, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya watau Mr. Mohammed Ahmed.

Wasu ma'aikata sun samu matsala da IPPIS

Cikin ma’aikata 59,201 aka tantance, 11,447 sun samu matsala da bayanansu a IPPIS.

Wannan ya jawo Folasade Yemi-Esan ta bada umarni a sake bude kafar IPPIS domin ayi la’akari da wadanda aka dakatar masu da albashinsu.

Da aka sake bada dama daga 16 zuwa 27 ga watan Oktoba domin tantance ma’aikatan da ba a tabbatar da bayanasu ba, wasunsu sun dace.

An yi hakan ne domin tabbatar da cewa ma’aikatan hakika kurum ake biya ta IPPIS.

Akanta Janar ya cigaba da biyan ma'aikatan

An aika sunayen wadanda aka tantance zuwa ofishin Akanta Janar na kasa, nan ta ke aka tabbatar da su da nufin a cigaba da biyansu.

Kara karanta wannan

Ministoci 10 da za su tashi da 86% na duka kudin da za a kashe a Najeriya a 2024

Wasu daga cikin wadanda ba a tantance da wuri ba sun fara samun albashinsu, This Day ta ce wasu kuma sai a Disamban nan za a biya su.

Ma'aikatan da aka tsaidawa albashin

Akwai ma’aikata 1,029 da aka samu kila-wa-kala a bayanansu, za a jira karin bayani daga ma’aikatunsu domin su cigaba da karbar albashi.

Ma’aikata 686 da gaba daya ba su iya zuwa wajen tantancewar ba sun sauka daga manhajar IPPIS, yanzu an tsaida albashin dukkansu.

An cire wasu daga IPPIS

A makon nan aka samu labari FEC ta janye matakin da aka dauka a baya na tilastawa manyan makarantu shiga cikin tsarin IPPIS.

Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin cire jami'o'i, kwalejojin fasaha da na ilimi daga IPPIS bayan shekara da shekaru ana korafi a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng