Duk ma’aikacin da baya cikin tsarin IPPIS ba zai sake samun albashi ba – Ministar kudi

Duk ma’aikacin da baya cikin tsarin IPPIS ba zai sake samun albashi ba – Ministar kudi

Duk wani ma’aikacin gwamnatin tarayya dake karkashin wata ma’aikata ko hukumar gwamnati da baya cikin tsarin biyan albashi na bai daya watau, IPPIS-Integrated Payroll and Personnel Information System ba zai sake samun albashinsa ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ministar kudi, kasafin kudi da tsare tsare, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka yayin da take gabatar da jawabi game da tsare tsaren kashe kudi na gwamnatin tarayya na matsakaici zango a Abuja, inda tace dokar za ta fara aiki ne daga watan Oktoba.

KU KARANTA: Tattakin Ashura: Yan Shia sun sake yin artabu da Yansandan Najeriya a Bauchi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan ta bayyana cewa wannan mataki ya zama wajibi domin toshe duk wasu ramuka da kudaden da gwamnati suke bi suna bacewa, tare da kokarin rage kudaden ayyukan yau da kulluma da gwamnati ke kashewa.

“Kudaden da ake kashewa a kan ma’aikata da yan fansho ya haura naira tirilyan 3, kuma kara hauhawa yake yi, amma gwamnati na daukan matakan rage wannan tashin gwauron zabi da kudaden suke yi, daga ciki akwai umarnin shugaban kasa na cewa daga watan Oktoba na 2019 dukkanin ma’aikatu da hukumomi sun shigar da ma’aikatansu tsarin IPPIS.” Inji ta.

Haka zalika ministar ta ce nan bada jimawa ba gwamnatocin jahohi zasu fara biyan kudin tallafi da gwamnatin tarayya ta basu a shekarar 2016, saboda a cewarta kudaden mallakin babban bankin Najeriya, CBN ce, don haka za’a cire daga kudadensu na wata wata da gwamnatin tarayya ke basu.

A wani labarin kuma, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta yanke hukuncin kwace wasu dimbin gwala gwalai mallakin tsohuwar ministar man fetur tare da mikasu ga gwamnatin tarayya.

Alkalin kotun, mai sharia Nicholas Oweibo ne ya yanke wannan hukunci a zaman kotun na ranar Talata, 10 ga watan Satumba sakamakon Diezani ta gagara bayyana ma kotu dalilinta na cigaba da mallakan gwala gwalan bayan EFCC ta shaida ma kotu cewa da kudaden sata aka sayesu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel