Bankin Duniya Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Farashin da Ya Kamata a Saida Fetur a Gidajen Mai

Bankin Duniya Ya Fasa Kwai, Ya Fadi Farashin da Ya Kamata a Saida Fetur a Gidajen Mai

  • Bola Ahmed Tinubu yana hawa kan mulki ya sanar da cire tallafin da aka saba biya a kan tallafin man fetur
  • Bankin duniya ya nuna akwai alamar tambaya game da janye tsarin, ana zargin har yanzu akwai rangwame
  • Alex Sienaert ya ce lissafinsu ya nuna litar fetur ta wuce N650, farashin asali zai iya haura N750 a kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bankin duniya yana ganin akwai alamar tambaya game da farashin litar fetur duk da gwamnati ta ce ta cire hannunta.

Ranar Laraba The Nation ta rahoto masanan bankin suna nuna cewa da alama har gobe gwamnatin tarayya ta na biyan tallafin mai.

Fetur
Shugaban Najeriya ya cire tallafin fetur Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Taron bankin Duniya a Najeriya

Alex Sienaert ya halarci wani taro da aka shirya domin tattaunawa a game da Najeriya da manufofin sabuwar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya laƙume rayukan aƙalla mutane 10 a babban titi a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban masanin bankin na Duniya ya halarci taron da aka yi a Abuja, ya ce ya kamata a rika saida duk litar man fetur ne kan N750.

Mista Alex Sienaert yake cewa idan aka duba farashin Dalar Amurka a kan Naira, za a fahimci lallai litar fetur ta kai N750 yau a kasuwa.

Sienaert yana zargin an dawo da tallafin fetur

“Idan mu ka kiyasta abin da ya kamata ya zama shi ne farashin man fetur, kuma mu ka yi lissafin cewa ana shigo da kaya ne a kan farashin canjin gwamnati, za a ga kamar kudin fetur bai yi daidai da farashin yanayin kasuwa ba, hakan ya nuna an dawo da wani bangaren tallafi.
Muna tunani ya kamata fetur ya zama N750, fiye da N650 da ‘yan Najeriya su ke biya.”

- Alex Sienaert

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun kuma ta’adi a Abuja, an yi garkuwa da mace da yaranta har da jariri

Babu shakka fetur ya wuce N650

Vanguard ta ce ba dole ba ne farashin ya tabbata kamar yadda Sienaert ya fada, a cewarsa kiyasi ne kurum da ya tabbatar da lita ta fi N650.

Bankin Duniya ya gamsu cewa shakka babu gwamnati ta cire hannunta wajen canjin kudi wanda hakan ya shafi farashin shigo da mai.

Ana kuka da tsadar fetur

Wani rahotonmu ya nuna mafi yawan al'ummar Najeriya su na faman kokawa a game da 'dan karen tsadar rayuwa da tashin kudin fetur.

Cire tallafin man fetur da aka yi ya jawo farashin fetur ya karu zuwa kusan N700 sannan kudin gas da ake saye domin yin girki ya tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng