Majalisar Rivers Ta Kori ’Yan Majalisu 25 da Suka Sauya Sheka, Fubara Ya Gabatar da Kasafin 2024
- Majalisar dokokin jihar Rivers ta ayyana kujerun wasu 'yan majalisu 25 matsayin "wofi" biyo bayan sauka sheka daga PDP zuwa APC
- Kakakin majalisar Edison Ehei da ke goyon bayan gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya yi amfani da kundin dokar Najeriya wajen daukar matakin
- A safiyar yau ne majalisar ta yi zamanta na farko a cikin fadar gwamnatin jihar biyo bayan fara rushe ginin majalisar da aka yi a safiyar Laraba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Rivers - Kakakin majalisar jihar Rivers, Edison Ehie ya wofantar da kujeru 25 na 'yan majalisun da suka zabi yin biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Wike.
Kakakin majalisar ya bayyana hakan a zaman majalisar na safiyar ranar Laraba, inda ya ce sashe na 109 (1) (g) da (2) na kundin dokar Najeriya ya ba shi ikon yin hakan.
Yan majalisu 25 da majalisar ta ayyana kujerunsu matsayin wofi, su ne suka sauya shekara daga PDP zuwa jam'iyyar APC a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rusa ginin majalisar dokokin jihar Rivers
Yan majalisar da ke biyayya ga Gwamna Siminalayi Fubara, sun yi zaman ne a fadar gwamnatin jihar da ke Fatakwa, inda gwamnan ya gabatar da kasafin 2024.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Gwamna Fubara ya ba mambobin majalisar wani matsugunni a gidan gwamnatin don gudanar da zamansu.
A safiyar yau ne Legit Hausa ta ruwaito maku cewa an fara rushe ginin majalisar dokokin jihar Rivers biyo bayan wata gobara da ta kama wani shashe na majalisar a ranar 29 ga watan Oktoba.
Fubara ya gabatar da kasafin 2024
Gwamna Siminalayi Fubara, ya isa majalsiar jihar Rivers don gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na jihar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan ya isa matsugunnin majalisar da ke a fadar gwamnatin jihar da misalin karfe 9 na safiya, wanda ya samu tarbar kakakin majalisar, Edison Ehie.
Fubara ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar, Tammy Danagogo, kwamishinan kudi, Isaac Kamalu, kwamishinan watsa labarai Joseph Johnson da wasu mukarrabansa.
Majalisar zartaswar jihar a zamanta na biyar a ranar Litinin, ta amince da Naira biliyan 800 matsayin kasafin kudin 2024 wanda su ke sa ran zai dawo da martabar jihar.
Asali: Legit.ng