Duk da Jerin Alkawura, 'Yan Tudun Biri Sun Kai Karar Gwamnati a Kotu Ana Neman N33bn

Duk da Jerin Alkawura, 'Yan Tudun Biri Sun Kai Karar Gwamnati a Kotu Ana Neman N33bn

  • Wani mutumi ya shigar da karar gwamnatin Najeriya saboda abin da ya faru da jama’a a kauyen Tudun Biri
  • Alhaji Dalhatu Salihu ya dauki hayar lauya zuwa babban kotun tarayya a garin Kaduna domin neman hakkokinsu
  • Lauyan da ya tsayawa wannan mutumi yana so kotu ta umarci gwamnati ta biya diyyar fiye da Naira biliyan 30

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kaduna - Mutanen kauyen Tudun Biri a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, za su yi shari’ar da gwamnatin tarayya a kotu.

Daily Trust ta ce al’ummar wannan kauye sun yi karar gwamnatin Najeriya a kotu a sakamakon T

Harin Kaduna
Tawagar Gwamnatin tarayya a Kaduna Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya v Tudun Birni a kotu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da sojojin da su ka yi wannan aiki, ya kuma yi alkawarin a gudanar da bincike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dira Kaduna kan kisan musulmai a bikin Maulidi, ya faɗi matsalar da aka samu tun farko

Sai dai hakan bai hana wasu mutanen wannan gari su shigar da kara a babban kotun tarayya da ke Kaduna domin neman hakki ba.

Mutumin garin Tudun Biri ya je kotu

Tun makon jiya Alhaji Dalhatu Salihu ya kai maganar zuwa gaban Alkali a madadin mutanen Tudun Biri ta hannun lauyansa.

Mukhtar Usman Esq ya ce mutanen wannan kauye su na neman a fitar da sanarwa a manyan gidajen jaridu domin a bada hakuri.

Lauyan ya ce sun je kotun tarayyan ne saboda dokar kasa ta ba kowa damar rayuwa, amma sojoji su ka kashe jama’a haka kurum.

Bukatar lauyan mutanen Tudun Biri

Daga cikon karar Mubakar Esq a kotu shi ne a ayyana kashe mutane fiye da 100 da sojoji su ka yi a matsayin keta alfarmar ‘yan kasa.

Sashe na 33 na kundin tsarin mulkin 1999 ya ba mutane damar rayuwa, sojoji sun kashe mutane fiye da 100 ta hanyar jefa masu bam.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Lauyoyin arewa fiye da 600 za su maka gwamnatin Tinubu a kotu, sun fadi dalili

Wani sashe na dokar kare hakkin Bil Adam na Afrika ya goyi bayan tsarin mulkin kuma dama gwamnati ta ce za ta biya diyyar rayuka.

Rahoton ya ce zuwa yanzu ba a tsaida lokacin da za a fara sauraron karar Mukhtar Usman Esq da gwamnatin tarayyar Najeriya ba tukuna.

IMN tayi zanga-zangar kisan Kaduna

An ji labari cewa kungiyar IMN ta ce dole a fito a bukaci ayi wa mutanen garin Tudun Biri adalci a kan kashe mutane da sojojin kasa su ka yi.

Mabiyan shi’an sun yi zanga-zanga domin gwamnati ta gano wadanda su ka yi aika-aikan, an kuma nemi ayi bincike domin gurfanar da sojojin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng