Ministoci 10 da Za Su Tashi da 86% na Duka Kudin da Za a Kashe a Najeriya a 2024

Ministoci 10 da Za Su Tashi da 86% na Duka Kudin da Za a Kashe a Najeriya a 2024

  • Ma’aikatar da ke gaba wajen samun kudi daga kasafin 2024 ita ce ta tattalin arziki da harkar kudi
  • Gwamnatin tarayya ta ware kudi masu yawa ga ma’aikatar tsare-tsare da kasafin kudi a badi
  • Bola Tinubu ya yi niyyar batar da biliyoyi a ma’aikatar tsaro na kasa da ma’aikatar Neja-Delta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kundin kasafin kudin da ke dauke da bayanan abin da ake so a kashe a Najeriya a shekarar 2024.

Da The Cable ta yi nazarin kasafin kudin na 2024 da kyau, an fahimci cewa wasu manya ma’aikatu 10 za su tashi da kaso mafi tsoka a ciki.

Kasafin kudi
Bola Tinubu da kasafin kudi Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

An warewa wadannan ma’aikatun tarayya N20.7tr daga cikin kasafin kudin na N24.07, hakan yana nufin su kadai za su samu har 86.3%.

Kara karanta wannan

Abba: Kasafin kudin Sarakuna 4 ya haddasa hayaniya tsakanin ‘yan Majalisar jihar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerin ma’aikatun da su ka fi samun kudi:

1. Ma’aikatar kudi

Ma’aikatar kudi da tattalin arziki ta samu N9.33tr a kasafin 2024. Mafi yawan kudin za su tafi ne a biyan albashi, N808.92bn aka ware domin ayyuka.

2. Ma’aikatar kasafi

N4.45 aka warewa ma’aikatar da ke shirya kasafin da sauran tsare-tsaren tattalin arziki. Ma’aikata za su ci N1.79tr, sannan za ayi ayyuka na N1.88tr.

3. Ma’aikatar tsaro

Idan an samu yadda ake so a majalisar tarayya, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta kashewa ma’aikatar harkar tsaro N1.58tr a shekara mai zuwa.

4. Ma’aikatar ilmi

Binciken ya nuna N1.44tr aka ware domin sha’anin ilmi ya bunkasa a kasar, amma N1.04tr zai tafi wajen albashi ne, watakila shiyasa ASUU ta ke korafi.

5. Ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a

Jaridar ta ce Farfesa Muhammad Ali Pate ya samu N1.23tr a kasafin kudin da aka tsata. Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kason zai karu nan gaba.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa Sun Gano Minista Za Ta Kashe Naira Biliyan 1 a Tafiya Zuwa Kasar Waje

6. Ma’aikatar harkokin ‘yan sanda

Abin da za a kashewa ma’aikatar ‘yan sanda a 2024 zai iya kai N938.74bn wanda mafi yawa za su tafi ne wajen biyan albashin jami’an tsaron kasar.

7. Ma’aikatar ayyuka

Daga cikin N657.23bn da aka warewa Dave Umahi, ana sa rai ma’aikatar ayyuka za ta kashe N612.85bn domin yin kwangilolin tituna da gadoji a jihohi.

8. Ma’aikatar cikin gida

A kasafin kudin shekara mai zuwa, N461.99bn za su tafi ga ma’aikatar harkokin cikin gida. Legit ta fahimci hakkokin ma’aikata ne za su cinye kusan 80%.

9. Ma’aikatar aikin gona

Domin ganin an samar da isasshen abinci daga gonaki, Sanata Abubakar Kyari zai so ma’aikatarsa ta kashe akalla N362.94bn a shekarar da za a shiga.

10. Ma’aikatar Neja Delta

Ma’aikatar da ta rufe goman farko ita ce ta harkokin Neja-Delta da za a kashewa N346.12bn. Abin mamaki, N18bn kadai aka yi tanadi domin ayyuka.

Kasafin kudin gwamnatin Kano

A matakin jihohi, ana da rahoto ‘yan Majalisar jihar Kano sun yarda gwamna Abba Kabir Yusuf ya kashe karin N24bn a shekarar nan da za ta kare.

Lawan Hussaini (NNPP) ya ce daga kasafin kudin ne za a inganta bangaren ilimi da na kiwon lafiya kuma a dauki nauyin masaratun da ke fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng