Abba: Kasafin Kudin Sarakuna 4 Ya Haddasa Hayaniya Tsakanin ‘Yan Majalisar Jihar Kano

Abba: Kasafin Kudin Sarakuna 4 Ya Haddasa Hayaniya Tsakanin ‘Yan Majalisar Jihar Kano

  • Kwarya-kwaryan kasafin kudi na shekarar 2023 ya samu amincewar Majalisar dokokin jihar Kano a makon nan
  • ‘Yan majalisar sun yi na’am da bukatar Abba Kabir Yusuf na kashe karin Naira biliyan 24 a shekarar nan ta 2023
  • An amince da bukatar Mai girma Gwamnan Kano bayan kasafin kudin masarautu ya jawo muhawara a majalisar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudi na shekarar 2023 a zaman da aka yi ranar Talatar nan.

Daily Trust ta tabbatar da ‘yan majalisar dokoki sun amince bukatar Mai girma Abba Kabir Yusuf na kashe karin N24bn a shekarar 2023.

Gwamnan Kano
Gwamna da Sarkin Kano Hoto: Abba KabirYusuf
Asali: Facebook

Gwamnatin Kano ta kashe N350bn a 2023

Gwamnoni su kan bukaci karin kudin kashewa kamar yadda aka yi a 2021. Matakin da aka dauka ya jawo gwamnati ta kashe N350bn a bana.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa Sun Gano Minista Za Ta Kashe Naira Biliyan 1 a Tafiya Zuwa Kasar Waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban masu rinjaye a majalisa, Lawal Husseini mai wakiltar Dala ya ce amincewa da kasafin zai bada damar yi wa mutanen Kano aiki.

Hon. Lawal Husseini yake cewa a haka gwamnati za ta bunkasa harkar ilmi da lafiya kuma a biya tsofaffin ma'aikatan da su ka yi ritaya hakkokinsu.

Rigima a kan kasafin kudin masarautun Kano

Sai dai ba haka nan aka amince da bukatar Abba Kabir Yusuf ba, sai da wata ‘yar hayaniya ta kaure tsakanin ‘yan majalisar na jihar Kano.

Aminiya ta ce ‘yan majalisar sun yi mamakin yadda aka nuna bambamci cikin kasafin kudin da aka warewa masarautu biyar da ake da su.

A yayin da gwamnati ta yarda a batar da N2.5m a masarautun Kano, Gaya, Rano da Bichi, an warewa masarautar Karaye N50m a shekarar nan.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano ya bayyana gaskiyar zaman Abba 'dan NNPP kafin hukuncin kotun koli

Da ‘yan majalisa su ka nemi jin dalilin haka, sai shugabansu Rt. Hon. Jibril Falgore ya nuna masarautar Karaye kadai ta iya kare kasafinta.

Sauran masarautun ba su iya gamsar da majalisar dokoki a kan yadda za su kashe miliyoyin da aka yi niyyar ware masu a kasafin bana ba.

A karshe an samu jituwa, har Tukur Muhamma Fagge ya gabatar da rahoton binciken ma’aikatun gwamnati da aka yi daga 2018-2020.

Shari'ar Abba v Gawuna a kotun koli

Ana da labari cewa ‘yan NNPP da Kankwasiyya sun dage da yin addu’o’i a jihohin Kudu da na Arewa bayan rashin nasara a kotunan baya.

Shugabannin jam’iyyar NNPP sun ce Bola Tinubu ya guji katsalandan a shari’ar Abba Kabir Yusuf da APC inda aka ba Nasiru Gawuna gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng