‘Yan Majalisa Sun Gano Minista Za Ta Kashe Naira Biliyan 1 a Tafiya Zuwa Kasar Waje
- Doris Uzoka-Anite ta yi tanadin akalla Naira biliyan 1 a matsayin kudin da za ta kashe zuwa wani taro a birnin Geneva
- Kwamitin hadaka na harkar kasuwanci da masana’antu a majalisa ya gano wannan wajen duba kasafin kudin 2024
- ‘Yan majalisar dattawa da wakilan tarayya sun bukaci jami’an gwamnati su rage kudin da ake kashewa wajen tafiye-tafiye
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A ranar Talata, Doris Uzoka-Anite ta bayyana gaban ‘yan majalisar tarayya ta kare kasafin kudin ma’aikatarta a shekarar 2024.
Ministar kasuwanci da masana’antu, Doris Uzoka-Anite ta amsa tambayoyi daga bakin kwamitin majalisa kamar yadda The Cable ta rahoto.
Majalisa na aiki a kan kasafin kudin 2024
Kamar yadda aka saba, Ministar ta shaidawa kwamitin cewa ta shirya kashe N905m kan hidindimu da N8.1bn wajen manyan ayyuka a 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kwamitin hadakan, Sanata Adams Oshiomhole ya yi wa kasafin kudin kallon kurilla, ya gano za a batar da N1bn a wata tafiya.
Rahoton ya ce Adams Oshiomhole mai wakiltar Edo ta Arewa a majalisar dattawa ya bukaci Ministar ta nemi yadda za ta rage kashe kudi.
An soki Minista a kan sirin kashe N1bn a Switzerland
Sanata Adams Oshiomhole ya yi tir da yadda aka ware har N1bn a tafiya guda da Ministar za ta yi zuwa birnin Geneva a kasar Switzerland.
“Na ga ki na niyyar zuwa birnin Geneva a shekara mai zuwa, kuma kin ware sama da Naira biliyan guda saboda tafiyar
Ba za mu cigaba da zuwa ketare da tulin jama’a ba. Ki yi amfani da kwararrun da ke cikin ofishinki domin a rage kashe kudi."
- Adams Oshiomhole
Ana so Minista ta duba alaka da Sin
Premium Times ta ce Oshiomhole ya kuma nemi jin alakar kasuwancin da ke tsakanin Najeriya da kasar Sin daga bakin Uzoka-Anite.
Tsohon shugaban kungiyar kwadagon yana ganin cewa ya kamata kasashen da ke shigo da kaya Najeriya su kafa manyan masana’antu.
Ministar kasuwanci ba ta zama a ofis
Uzoka ta nuna ba su da wannan bayanan, amma Oshiomhole bai yarda da abin da ta fada ba, ya kuma bukaci Ministar ta rika zama a ofis.
Sanatan ya ce kullum Ministar tana BOI, sai ta nuna masa ana gyaran ofishinta ne kuma za ta iya yin aikinta daga ko ina ne a kasar nan.
Sababbin tsare-tsare a CBN
Rahoto ya zo cewa manoman da aka ba bashi domin a samu isasshen abinci za su dawo da kudin da su ka karba a karkashin tsarin CBN.
Sabon gwamnan da aka nada a CBN watau Micheal Yemi Cardoso babu ruwansa da duk harkokin da ba aikin banki da kuma karfafa Naira ba.
Asali: Legit.ng