Harin Bam Kan Masu Maulidi: Iyalan Mutanen da Suka Rasu Sun Maka FG Kara a Kotu, Sun Fadi Bukatunsu

Harin Bam Kan Masu Maulidi: Iyalan Mutanen da Suka Rasu Sun Maka FG Kara a Kotu, Sun Fadi Bukatunsu

  • An maka gwamnatin tarayyar Najeriya Najeriya a gaban kotu kan harin da sojoji suka kai a ƙauyen Tudun Biri
  • Iyalan mutum 53 da suka rasa ransu a sakamakon harin ne suka shigar da gwamnatin tarayya ƙara a babbar kotun tarayya da ke Kaduna
  • Iyalan ta hannun lauyansu sun buƙaci kotu ta tilasta sanya gwamnatin tarayya biyan diyyar N33bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Iyalan mutum 53 da suka rasu a sakamakon harin da sojoji suka kai a jihar Kaduna sun kai ƙarar gwamnatin tarayya, inda suka bukaci a biya su diyyar Naira biliyan 33.

Kimanin mutane 100 ne ake fargabar sun rasu a wani hari ta sama da wani jirgin soji ya kai a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna a ranar 3 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dira Kaduna kan kisan musulmai a bikin Maulidi, ya faɗi matsalar da aka samu tun farko

An maka FG kara kan harin Tudun Biri
Shugaban sojin kasa yayin ziyarar ta'aziyya a kauyen Tudun Biri Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Tuni dai gwamnatin Najeriya ta ɗauki alhakin lamarin inda ta aike da tawaga biyu karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da babban hafsan sojin ƙasa Taoreed Lagbaja domin kai ziyara ƙauyen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan waɗanda suka rasu sun shigar da ƙara?

Amma, wata ƙarar kare haƙƙin ɗan Adam da aka shigar a babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta hannun wakilin iyalan, ta lissafo gwamnatin tarayyar Najeriya, da babban lauyan gwamnatin tarayya, da kuma babban hafsan soji a matsayin waɗanda ake tuhuma.

Jaridar Premium Times wacce ta ga takardun ƙarar a ranar Talata, ta ce mai shigar da ƙara, Dalhatu Salihu, ya shigar da ƙarar ne a ranar 8 ga watan Disamba.

A cikin ƙarar ya buƙaci a kare ƴancin yin rayuwa da waɗanda harin ya ritsa da su, Sani Sulaiman, Salima Abdurrahman, Ibrahim Idris, da wasu mutum 50.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa kai cikin Abuja, sun tafka mummunar ɓarna tare da kashe jami'in tsaro

Lauyan wanda ya shigar da ƙarar, Mukhtar Usman, ya bayyana ƙarar a kan sassan da suka dace na dokokin aiwatar da hakkin ɗan adam na 2009, kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma Yarjejeniya ta Afirka kan ƴancin ɗan Adam.

Menene buƙatunsu a cikin ƙarar?

Ƙarar ta buƙaci kotun ta bayyana "harin halaka mutane ta hanyar jefa bam kan mutanen da ke bikin mauludi" ya keta ƴancin marigayan na yin rayuwa" kamar yadda aka tanada a kundin tsarin mulki.

Mai shigar da ƙarar ya buƙaci kotun da ta ayyana harin na sojoji "haramtacce, wanda ya saɓa doka kuma ba bisa ƙa'ida ba."

Ya buƙaci N33bn a matsayin diyya wanda gwamnatin tarayya za ta biya ga iyalan mutanen da suka rasa ransu.

A wata buƙatar, mai shigar da ƙara ya bukaci kotun da ta bayyana kudin ruwa na kaso 10% cikin 100% a duk shekara daga ranar da za ta yanke hukunci har sai an kammala biyan kuɗin hukuncin da ta yanke.

Kara karanta wannan

Mako ɗaya bayan jefa bam a Kaduna, 'yan bindiga sun ƙara yin mummunar ɓarna kan bayin Allah

Hakazalika ya buƙaci gwamnati ta nemi afuwar jama'a game da kashe-kashen wacce za a buga a manyan jaridu na ƙasar nan.

Tinubu Ya Gargadi Sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya da su ƙauracewa jefa bam kan fararen hula, ya ce irin hakan ba za ta sake faruwa ba.

Shugaban ƙasan ya yi wannan gargaɗin ne a Maiduguri a yayin bikin bude taron hukumar tsaro ta rundunar soji na shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng