Kwalejin Kiwon Lafiya: Ministan Tinubu Ya Roki Dalibai da Likitoci Su Shiga Aikin Soja

Kwalejin Kiwon Lafiya: Ministan Tinubu Ya Roki Dalibai da Likitoci Su Shiga Aikin Soja

  • Gwamnatin tarayya ta neman likitoci da daliban da ke karatun kiwon lafiya da su shiga aikin soja don bunkasa lafiyar jami'an sojin kasar
  • Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce gwamnati na daf da gina kwalejin kiwon lafiya ta sojoji, don akwai bukatar karin ma'aikata
  • Matawalle ya ce za a gina babban asibiti a Abuja wanda zai dauke dukkanin bukatar rashin lafiyar jami'an soji da suka yi ritaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta roki daliban kiwon lafiya da kwararru a fannin lafiya da su shiga aikin soja don kara yawan masu aikin jinya da ke duba sojojin kasar.

Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, a ranar Talata ya ce shigar malaman kiwon lafiya aikin soja zai rage yawan sojojin da ke fitar kasar wajen neman aiki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya: "Kar ku kuskura ku kara jefa bam kan fararen hula"

Ministan tsaro/Rundunar soji
Matawalle ya ce samun karuwar dalibai da likitoci a aikin soja zai cika muradin Tinubu na gina kwalejin kiwon lafiya ta sojoji. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Matawalle wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma'aikatar, Dr. Abubakar Kana, ya fadi hakan a wani taro masu ruwa da tsaki na hukumar tsaro a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnati za ta gina babban asibiti a Abuja wanda zai dauke dukkanin bukatar rashin lafiyar jami'an soji da suka yi ritaya a fadin kasar, rahoton The Nation.

Ministan ya ce samun malaman jinya a aikin soja zai taimaka wajen ganin gwamnati ta cika muradinta na gina kwalejin kiwon lafiya ta sojoji.

A cewarsa:

"Daga kokarin gwamnati shi ne kara yawan sojoji da ke aiki a fannin kiwon lafiya don duba marasa lafiya, neman shawarwari da masu neman kwarewa.
"Tuni dai aka gama shiri na kara gina wasu dakuna da za su dauki akalla gadaje 100 na marasa lafiya a asibiti soji na 44 da ke Kaduna, don dalibai masu son sanin makamar aiki."

Kara karanta wannan

Sanatoci sun burge, sun ba da albashinsu gaba daya ga 'yan maulidin da harin soji ya shafa

Matawalle ya kuma koka kan yadda sojoji ke tafiya kasashen waje neman aiki, inda ya ce hakan ta sa suke neman daliban kiwon lafiya daga jami'o'i su shiga aikin soja.

Ya kuma nuna muhimmancin da ke akwai na samar da hukumar inshorar lafiya ta jami'an soji da za ta bunkasa lafiyar jami'an soji masu aiki da wadanda suka yi ritaya, har ma da iyalansu.

Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya kan harin Kaduna

A wani labarin, shugaban kasa Bola Tinubu ya gargadi sojojin Najeriya da su kauracewa kai hare-hare kan fararen hula, da kuma kai wa sauran jami'an tsaro hari, Legit Hausa ta ruwaito.

Tinubu na martani ne kan harin bam da sojoji suka kai Kaduna da ya kashe sama da mutum 100 da kuma farmakar ofishin 'yan sanda a Adamawa da ya yi silar ajalin wani sufeta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.